Daga Mahdi M. Muhammad,
Shugaban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, ya bayyana cewa, rukunin ayyuka na musamman na (115 SOG) da ke fatakwal zai dauki karin matsayi a bangaren tsaro na teku domin zai kasance daya daga cikin sansanonin jiragen sama na musamman guda 3 da aka tura zuwa Benin a matsayin wani bangare na gudanar da jiragen ruwan Nijeriya (NIMASA) na ‘Deep Blue Sea Project’, da nufin magance matsalar rashin tsaro da aikata laifuka a cikin yankunan Nijeriya da yankin tattalin arziki (EEZ).
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar, 20 ga watan Janairun 2021, yayin da ya ke ba da na’urar binciken lafiya ta ‘Computerized Tomography Scan’ (CT Scan) da kuma wani rukunin masauki mai dakuna 30 ga sojojin sama a sansanin sojin saman Nijeriya (NAF) da ke fatakwal.
Daramola ya kara da cewa, Samun da kuma sanya kayan aikin na ‘CT Scan’ din a ‘NAF Reference Hospital Port Harcourt’ an aiwatar da shi ne da nufin bunkasa ayyukan kiwon lafiya ga ma’aikata da iyalansu da kuma al’ummomin da ke karbar bakuncin NAF.
Ya ci gaba da cewa, an sanya sabon na’urar ‘CT Scan’ ne da kyakkyawar niyya, yayin da ake inganta makarantar sakandaren Sojin Sama (AFSS) zuwa makarantar sakandare mai cikakken Iko tare da gina dakunan kwanan dalibai mata da maza a halin yanzu. A cewarsa, “NAF ta kasance tana bayar da tallafin da ake matukar bukata ta sama a wurare daban-daban na yaki da ta’addanci a duk fadin kasar nan, inda ‘115 SOG’ ke taka muhimmiyar rawa. Dangane da muhimmancin rawar da jami’ai maza da mata na 115 SOG ke takawa wajen cimma kyakkyawar manufa, NAF ta kara himma don magance kalubalen rashin isassun matsugunan jami’ai maza da mata, yayin daukar matakai don inganta wuraren samar da ilimi da kiwon lafiya don ma’aikata da iyalansu”.
Don haka Air Marshal Abubakar ya yaba wa Kwamandan Sojojin Sama da ke Kula da ‘Tactical Air Command’ (AOC TAC), Air Vice Marshal (ABM) Olusegun Philip, da kuma Kwamandan 115 SOG, Group Captain Dooyum Laha, da jami’an sa kan kokarin da suka yi na tabbatar da tsaro kasar. Ya bayyana cewa, hedikwatar NAF, a nata bangaren, za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da ya dace don baiwa rukunin damar yin aiki yadda ya kamata.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a kan gudummawar NAF na ci gaba da yaki da cutar korona, shugaban ya bayyana cewa, rundunar za ta ci gaba da samar da tukunyar iskar shaka na ‘Likuid Odygen’ (LOD) daga wurarensu a rukunin ‘103 Strike Group’ (103 STG) Yola, zuwa cibiyoyin kula da cutar da ke babban birinin tarayya Abuja da sauran wurare a duk fadin kasar.
Ya kara da cewa, sansanin da suke samar da tukunyar iskar shakar ‘103 STG LOD’ na samar da lita 1,000 na LOD a cikin awanni 24, wanda hakan ya wuce karfin bukatun NAF na ayyukanta na sama da kuma amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na fadin kasar baki daya. Saboda haka, wajen samar LOD din tun a lokacin da cutar ta fara, suna samar da iskar odygen na asibiti don rarrabawa zuwa cibiyoyin kula da cutar da wuraren kebe masu cutar, a matsayin wani bangare na matakan tallafawa gudanar da manyan lamuran korona.
A jawabinsa na maraba, AOC TAC, yayin da yake mika godiyar sa ga shugaban kan ayyukan da ake yabawa a kasa, ya ce, babu shakka CT Scan zai inganta samar da ingantaccen kiwon lafiya ga ma’aikatan NAF da dangin su da kuma al’ummomin da suka karbi bakuncinsu a cikin jihar Ribas, da kuma dukkan yankin Neja Dalta na kasar. A cewarsa, “sadaukarwar da shugaban ya yi don samar da ababen more rayuwa don kyakkyawan aiki da jin dadin ma’aikatan NAF, musamman a sansanin NAF da ke fatakwal, abin birgewa ne kwarai da gaske”. Don haka AOC ya sake ba wa shugaban tabbacin dagewa da sadaukar da ma’aikata don yin iya bakin kokarinsu wajen bayar da gudummawa ga zaman lafiya da tsaron kasar.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da kwamandan rundunar hadin gwiwa, ‘Operation DELTA SAFE’ (OPDS), Rear Admiral Akinjide Akinrinade, da shugabannin sansanin NAF tare da Kwamandojin rundunar da Shugabannin hukumomin tsaro a Fatakwal. Kafin su bar Fatakwal, shugaban sojin saman ya kuma binciki aikin gine-gine da ke gudana a AFSS na fatakwal da kuma wasu ayyukan a sansanoni.