Daga Mahdi M. Muhammad,
A ci gaba da kokarin inganta ayyukanta na yaki da ‘yan bindiga da sauran masu aikata ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan, Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), sun shirya kafa wani filin gudanar da ayyuka (FOB) a Funtua, Jihar Katsina.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, an bayyana hakan ne a ranar, 7 ga Janairu 2021, ta hannun shugaban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadique Abubakar, yayin ziyarar dubawa zuwa inda FOB din take.
Shugaban, wanda ya samu rakiyar ziyarar tare da Shugabannin Sojojin sama masu jagorantar horarwar da kwamandan ayyuka na musamman da kuma wasu Shugabannin sansanoni da daraktoci daga hedikwatar NAF, Kuma dukkan su sun samu karbuwa a filin FOB din daga Sarkin maskan Katsina, Dakacin Funtua, Alhaji Idris Sambo, da kuma Shugaban gudanarwa na karamar hukumar Funtua, Alhaji Umar Mustapha, wadanda dukkansu suka nuna farin cikinsu da ci gaban.
Da yake zantawa da manema labarai bayan duba wurin, Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, NAF da ke aiki tare da ‘yan uwa maza da mata da sauran hukumomin tsaro, za ta cigaba da jajircewa ba tare da wata matsala ba don tabbatar da tsaro da lafiyar dukkanin ‘yan Nijeriya, a duk inda suke zaune. Ya kuma yi karin haske da cewa, sabon FOB din, idan aka kammala shi, zai rage lokacin mayar da martani na jirgin saman kai hari na NAF zuwa abubuwan gaggawa a yankin, ta haka zai kawo tsaro kusa ga mutane. Don haka ya nemi goyon baya da hadin kan mutanen yankin domin samun nasarar tashi daga aikin.
Yayin da yake bayyana cewa tsaro aiki ne na kowa da kowa wanda ke bukatar sa hannun dukkan ‘yan kasa, shugaban a takaice ya karfafa gwiwar dukkan mutane a yankunan da abin ya shafa da su samar da bayanan da suka dace wadanda zasu taimakawa hukumomin tsaro wajen tabbatar da kariyarsu. Air Marshal Abubakar, yayin da yake mika godiyar sa ga Gwamnatin jihar Katsina kan ware filin ga NAF, ya kuma umarci Daraktan ayyuka da masu tallafawa NAF da su fara aiki ba tare da Bata lokaci ba, zuwa ga kammala aikin cikin sauri.