NAF Ta Karfafa Kawancenta Da Kasar Hungary Don Yakar Ta’addanci A Nijeriya

NAF

Daga Mahdi M. Muhammad,

A yayin da rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) da ‘yar uwarta ta rundunar sojin kasa ke ci gaba da samun nasarori da dama a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, sojojin sun shirya kara kawance da kasar Hungari a fagen horar da matukan jirgin sama, da aiki da kuma kula da bayanan sirri, Kama kyamarorin, sa ido da kuma sake gano su (ISR), da ma wasu muhimman wurare na kwarewa.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, an bayyana hakan ne a ranar, 22 ga watan Janairun 2021, ta hannun shugaban hafsan sojan sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, yayin da ya karbi bakuncin karamin janar din kasar Hungary a Nijeriya, Mista Endre Peter Deri, da kuma babban jami’in kamfanin kera jiragen saman na ‘Hungarian Magnus Aircraft Manufacturing Factory’, Mista Laszo Boros, a Hedikwatar NAF da ke Abuja.

Da yake magana yayin ziyarar, shugaban ya bayyana cewa, bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da na bangarori daban-daban don yaki da ta’addanci ya zama dole saboda yanayin ta’addanci a duniya da kuma mummunar tasirin da yake da shi ta fuskar kaurar jama’a saboda tilasta yin hijira da kuma bata tattalin arziki da rikice-rikice, idan ba a magance su da kyau ba.

Ya kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin NAF da Hungary zai ba NAF damar yin amfani da kwarewar da ake samu a Hungary don magance wasu kalubalen fasaha da runsunar ke fuskanta a halin yanzu yayin gudanar da ayyukanta.

Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, NAF a shirye take ta tura tawaga zuwa Hungary don tantance damar da ake da ita ta jirgin sama da kuma mallakar kayan aiki, bunkasa iyawar dan adam da kuma bincike da ci gaban (R&D), a tsakanin sauran bangarorin hadin gwiwa. YA ce, “Kamar yadda kuka sani muna yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso gabas, kuma jirgin da masana’antar ta kera ta Hungary Magnus, wanda ke da karfin ISR, zai yi amfani wajen kara darajar abin da muke yi a Arewa maso gabas da sauran wuraren aiki.”

Ya nuna wasu fannoni da dama wadanda suka hada da horas da matukan jirgin yaki, masu fasahar jirgin sama da injiniyoyi tare da bunkasa karfin aiki da kuma kula da yawan kudaden ISR da kuma nazarin fasahar ISR.

Tun da farko, babban jami’in Kamfanin masana’antun kere-keren Magnus na kasar Hungary, Mista Laszo Boros, ya bayyana cewa, ziyarar na nufin nemo hanyoyin da za a karfafa kawancen dabarun hada jiragen sama da hada-hadar kayan aiki gami da kara karfin gwiwa.

Ya bayyana cewa, Kamfanin a shirye yake ta samar da hanyoyin magance matsalar wanda zai tallafawa ayyukan NAF a yaki da ta’addanci da sauran ayyukan ta’addanci. Haka zalika, karamin janar din Hungary, Mista Endre Peter Deri, ya bayyana shirye-shiryen zurfafa kawance da NAF, yana mai cewa, za ta kara inganta alakar da ke akwai tsakanin Nijeriya da Hungary ta fannin bunkasa iya aiki.

Wadanda suka halarci ziyarar sun hada da Shugabannin reshen hadikwatar NAF da sauran manyan hafsoshin NAF.

Exit mobile version