Daga Mahdi M. Muhammad,
A wani bangare na gudummawar da ta ke bayarwa ga kokarin Gwamnatin tarayya na kula da annobar korona a karo na biyu, Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) a ranar, 7 ga Janairu 2021, ta raba karin tukunyar iskar shaka ‘Likuid Odygen’ (LOD) kyauta zuwa asibitoci da wuraren kebewa masu cutar, a Abuja.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, sabbin wadanda suka ci gajiyar wannan karin rukunin sun hada da asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja, Gwagwalada da kuma sashin Kula da ayyukan gwamnati a Abuja, wadanda suka ci gajiyar rukunin farko da aka raba a watan Satumbar 2020.
Tukunyar iskan, wanda kamfanin ‘NAF LOD Plant’ ta samar a rukunin ‘103 Strike Group’ (103 STG) da ke Yola, an matsar dasu zuwa ‘NAF C-130 Hercules’ ne, kuma aka dauke shi zuwa Filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnmadi Azikiwe, Abuja kuma an mika shi ga wadanda suka amfana daga hannun kwamandan ma’aikatar lafiya (CMS), Air Commodore Gideon Bako, wanda kwamandan asibitin 063 na NAF Abuja ya wakilta, Group Captain Muzzammil Muhammed.
A nasa bangaren, daraktan sashin kiwon lafiya na asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, Mista Nathan Yatufate, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, ya nuna jin dadinsa da wannan karramawar da NAF din ta yi, yana mai cewa, iskar shakar ta taimaka sosai wajen ceton rayukan masu cutar da dama a cikin ‘yan kwanakin nan.
A halin yanzu, NAF, a ranar 6 ga Janairu 2021 ta ba da silinda na LOD zuwa babban asibitin gundumar Maitama, Abuja don kula da marasa lafiya na korona. Shugabannin asibitin sun godewa NAF saboda samar da iskar, wanda a cewarsu, har yanzu shine abu mafi muhimmanci da ake bukata wajen kula da marasa lafiya masu cutar korna a asibitin.