Bello Hamza" />

NAFDAC Ta Gargadi Mata Kan Yin Amfani Da Kayan Kawalliya Da Aka Kawo Daga Malesiya

Hukumar NAFDAC ta gargadin al’ummar kasar musamman mata akan amfani da kayan kwalliya da aka haramta amfani da su wadanda ake shigo da su daga kasar Malesiya.

Kayyakin da aka haramta sun hada da manshafawa na Sifu Kunyit Day Cream, Sifu Kunyit Night Cream and JJ Skincare da kuma Glowhite Night Cream, bayani ya kuma nuna cewa, ma’aitakan lafiya na kasar ta haramta mu’amala da kayan kwalliyar.

Farfesa Mojisola Adeyeye, shugabar hukumar, ta bayyana haka a sanarwa da ta raba a manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ta bayyana cewa, an gano cewa kayayyakin kwalliyar suna kunshe da wasu sinadarai masu cutar da mutane da suka hada da hydrokuinone, tretinoin, betamethasone balerate da kuma mercury wanda za su iya haifar da mastala ga fatar jiki da kuma lalata koda da kuma haifar da kansar fata.

Ta kuma kara da cewa, Man shafawa na  Sifu Kunyit Night na kunshe da sinadarin mercury da betamethasone 17-balerate, haka kuma manshafawar Sifu Kunyit Day Cream kuma na kunshe da hydrokuinone, tretinoin da betamethasone 17-balerate, yayin da kuma man shafawar JJ Skincare Glowhite Night cream yana dauke da sinadarin hydrokuinone, wadanda kuma duk suna cutar da jikin dan adam.

Adeyeye ta kuma kara da cewa, amfani da kayan kwalliyar na iya haifar da matsala ga kwakwalwa jarirai da ba a kai ga haihuwarsu ba.

 

Exit mobile version