NAFDAC Ta Garkame Gidajen Burodi 24 A Jihar Borno

 

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta garkame gidajen burodin 24, wadanda ke gudanar da sha’anin kasuwancin su ba bisa ka’ida ba, a birnin Maiduguri ta jihar Borno.

Furucin daukar matakin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Nasiru Mato, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Bugu da kari kuma, shugaban hukumar NAFDAC din ya bayyana cewa sun dauki matakin rufe gidajen burodin sakamakon rashin cika sharudda da ka’idojin da hukumar ta shimfida, sannan da kin sabunta takardun lasisin su.

Ya ce sun garkame wasu daga cikin gidajen burodin ne ta dalilin rashin tsabta da gyara muhallan da suke gudanar da sana’ar biredin.

Har wa yau kuma, ya bayyana wasu daga cikin gidajen burodin da al’amarin ya shafa, wadanda suka kunshi gidan biredin Nurul Aini da Nice Bread hadi da D Boss, sai Sabe the Nation da Albarka, Eber-Nice tare da Aljazeera, da makamantan su.

“haka zalika kuma wasu daga cikin su ba su riga sun yi rijista da hukumar NAFDAC ba. Kawai suna gudanar da aikin su barauniyar hanya; ta hanyar amfani da sitikar bogi da suna da adireshi”.

“Akwai kimanin gidajen burodi 300 a jihar Borno, kuma mun yi amfani da hanyoyi daban-daban domin wayar da kai dangane da tabbacin samun hadin kai wajen bin doka da tsari, wanda ta hakan ne zai bamu damar gano bara-gurbi kuma domin kare lafiyar jama’a”. Inji shi.

Exit mobile version