Daga Khalid Idris Doya,
Hukumar da ke danya ido kan ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) ta garkame kamfanonin harhada magungina guda shida bisa rashin maida hankali kan tsafta a harkokinsu, kamar yadda kamfanin Dillacin Labarai ta kasa NAN ta nakalto.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NAFDAC, Mista Sayo Akintola, shi ne ya bayyana matakin a madadin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.
Ya ce wannan matakin na daga cikin manufofin hukumar na tabbatar da tsaftace inganci abinci da maguna ne ta a fadin kasar nan.
“Wadannan kamfanoni duk da irin gargadin da aka yi musu, sun gaza bin tsaftataccen tsarin gudanar da ayyuka na Good Manufacturing Process (GMP) domin tabbatar da tsaftar magunguna.”
Kazalika, shugabar ta koka kan yadda kamfanonin, wadanda na cikin gida ne, suka gaza bin ka’idoji marasa tsauri na kiyaye tsafta da ingancin kayayyakinsu.
Jami’in ya nanata cewa za su ci-gaba da tabbatar da sanya ido kan kamfanonin da su ke fadin kasar nan domin tabbatar da ingancin abinci da maguna.