Connect with us

LABARAI

NAFDAC Ta Kwace Jabun Magunguna A Jihar Delta

Published

on

Hukumar kula da lafiyar abinci ta kasa, (NAFDAC), ta kwace wasu kayayyakin da ba su da rajista a Asaba, Jihar Delta.
Daraktan hulxa da jama’a na hukumar, Dakta Abubakar Jimoh, ne ya faxi hakan a Abuja, ranar Asabar.
Jimoh ya bayyana cewa, daga cikin kayayyaki marasa rajistan da suka kwace akwai maganin kwari da suka kai Naira 250,000, ya kara da cewa, sun kwato su ne daga masu tallan su a kasuwar Ogbeogonogo.
Ya ce, kayayyakin na farko an kwace su ne a wani zagaye da hukumar ta yi a ranar 16 ga watan Agusta.
Kakakin hukumar ya ce, sun kwace magungunan gargajiya masu yawa daga masu tallan a Okpanam kusa da Asaba, a karamar hukumar Oshimili ta Arewa.
Ya bayyana cewa, wasu kayayyakin da suke da rajistan karya na hukumar ta NAFDAC, duk an kwace su daga wata mata mai suna Faith Onyinyechi, a Unguwar Obodogba.
Jimoh ya ce, hukumar ta NAFDAC a halin yanzun ta fi karfafa da kowane lokaci a baya, kuma a shirye take da ta raba kasuwannin kasar nan da duk wasu jabun kayayyaki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: