CRI Hausa" />

Nagartaccen Tsarin Siyasa Ya Sa Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Sosai A Kokarin Yakar Cutar COVID-19

Robert Lawrance Kuhn, shi ne shugaban asusun Kuhn na kasar Amurka, ya gaya ma manema labaru na kasar Sin cewa, yana da karfin gwiwa kan cewar kasar Sin za ta iya kawar da cutar COVID-19 a gida, saboda tsarin siyasa na kasar Sin ya ba ta damar daukar kwararan matakai don neman kawar da cutar COVID-19 cikin sauri.
Hakika sauran masanan kasashe daban daban suna da ra’ayi daya da na mista Kuhn, inda suke kallon yadda kasar Sin ke zama karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, a matsayin wani fifiko da kasar Sin ke da shi a fannin tsarin siyasa, da na kula da kasa, kuma wani muhimmin dalilin da ya sa kasar ke iya shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri.
Tun farkon wannan shekarar da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira wasu taruka don tabbatar da manufofin da za a dauka don tinkarar cutar COVID-19, inda ya jaddada wajibcin ba da muhimmanci ga batun da ya shafi rayuka da lafiyar jama’a.
Bisa umarnin da shugaban ya bayar, hukumomi na sassa da matakai daban daban na kasar Sin sun gabatar da jerin matakai, don kokarin tinkarar cutar COVID-19 cikin tsari, ta wasu dabaru da suka dace.
Yayin da ake fama da cutar dake yaduwa cikin sauri, kusan dukkan kasashe daban daban suna fuskantar matsaloli kamar karancin jami’an lafiya, da kayayyakin kandagarkin cutar, da rashin isassun gadajen kwantar da marasa lafiya, da dai sauransu. Sai dai kasar Sin ta yi nasarar daidaita wadannan matsaloli, bisa kwarewarta a fannin jagorar jama’a da neman samun hadin gwiwarsu. Don taimakawa wuraren da yanayin yaduwar cutar ya fi kamari, kasar Sin ta tura jami’an lafiya fiye da dubu 42 zuwa lardin Hubei da birnin Wuhan, tare da kafa wasu asibitocin wucin gadi a can. Kana kamfanonin kasar sun yi kokarin maido da ayyukansu, don samar da marufin baki da hanci, da kayan kariya da ake bukata. Sa’an nan jama’ar lardin Hubei sun samu damar samun jinya a wadannan asibitoci kyauta, inda aka sanya kamfanonin inshora da gwamnati biyan dukkan kudin da ake bukata wajen ceton rayukan jama’a.
Matakan da kasar Sin ta dauka a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 sun burge wata marubuciyar kasar Amurka mai suna Sara Flounders matuka, har ma ta rubuta cewa, “Wadannan matakai sun nuna mana halayyar musamman ta tsarin gurguzu, wato a lokacin da ake fuskantar barazana, wata kasar dake karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis za ta iya yanke shawara ba tare da la’akari da moriya ko wata riba ba, abubuwan da aka fi mai da hankali karkashin tsarin jarin hujja.

(Bello Wang)

Exit mobile version