Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Nagartar Kasar Sin: Dalilin Da Ya Sa Kasashen Duniya Ke Goyon Bayan Manufofinta

Published

on

A daidai lokacin da wasu kasashe ‘yan tsiraru ke tada jijiyoyin wuya dangane da matakin majalisar dokokin kasar Sin na zartar da dokar tsaron kasa a kan yankinta na musamman na Hong Kong, ’yan siyasa da gwamnatocin kasashe da dama, ciki har da na Afrika, sun nuna goyon bayansu ga matakin na kasar Sin.

A jiya Litinin, yayin ganawar jakadan kasar Sin Zhou Pingjian da ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama, Ministan ya ce Nijeriya na goyon bayan kasar Sin ta aiwatar da manufar “kasa daya, mai tsarin mulki biyu” a kan yankin musamman na Hong Kong, yana mai cewa, batun da ya shafi HongKong, batu ne na cikin gidan kasar Sin.
Sanin kowane cewa yankin musamman na Hong Kong, wani bangare ne da ba zai iya ballewa daga babban yankin kasar Sin ba, kuma tun bayan dawowar Hong Kong babban yankin a ranar 1 ga watan Yulin 1997, duk wani batu da iko da hakkokinsa, suka koma hannun kasar Sin.
Tushen huldar Sin da kasashen waje, ya dogara ne kan amincewa da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”. Ban da haka, kasar Sin kan nanata cewa, a cikin huldarta da kasashen ketare, babu danniya ko sharadi ko katsalandan cikin harkokinsu na cikin gida. Kamata ya yi, duk wani batu na cikin gida, ya zama ikon kasa ba tare da wasu kasashe sun tsoma baki ba. Wannan manufa ta kasar Sin, ta kasance shimfidar da ta kyautata tare da kara zurfafa huldarta da kasashen ketare. Kuma ta kasance dalilin da ya sa galibin kasashe ke martaba dukkan manufofin da ikonta a kan yankunanta na musamman.
Babu wata kasa a duniya da ta san ciwon kanta, da za ta nade hannu tana kallo ana yi wa muradu da tsoro da kwanciyar hankali da ’yancinta karan tsaye. A cewar Ofwono Opondo, kakakin gwamnatin kasar Uganda, tsaron kasa shi ne tubulin kasancewar dukkan kasashe a duniya, kuma kare tsaron kasa bisa doka, cikakken iko ne na dukkan kasashe, don haka ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga matakin kasar Sin. Haka zalika, jami’an gwamnatoci da masana daga kasashe daban daban, ciki har da Niger da Mali da India da Columbia da sauransu, dukkansu sun goyi bayan kasar Sin kan matakin da ta dauka, suna masu cewa, ya dace da kundin tsarinta, kana batu na cikin gidanta da bai kamata a tsoma baki a ciki ba.
Har kullum, kasar Sin na rajin tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan duniya, inda ta kan yi kira ga kasa da kasa da su daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen dake fama da rikici, da samar da maslaha bisa yanayin da ya dace da su da kuma girmama cikakken ’yancinsu. A irin wannan lokaci, kamata ya yi a taru a mara mata baya, a kuma karfafa mata gwiwar tabbatar da tsaro da oda a yankunanta, maimakon yi mata katsaladan da yunkurin kara tada kurar da take kokarin yayyafawa ruwa.
Baya ga haka, Sin kasa ce da ta kan sanya muradun jama’arta sama da komai. Kana tabbatar da kare lafiya da tsaronsu, abu ne da ba za ta yi wasa da shi ba, don haka ba za ta taba aiwatar da abun da zai musguna ko take hakkokin al’ummarta ba. Bugu da kari, me zai sa ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaro a dukkan yankunanta, a matsayinta na kasar da ta san ciwon kanta kuma take himmantuwa wajen kare al’ummominta?
Hakika su ma masu ganin baikenta, fakewa kawai suke da batun domin cimma wasu bukatunsu, ba tare da sun yi la’akari da yanayi da muradu da makomar yankin ba. (Fa’iza Mustapha)

Advertisement

labarai