A cikin shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, al’ummar kasar Sin ta samar da kyakkyawan tarihi da al’adu, tare da tunanin da’a na kanta. Abubuwa mafi kyau dake cikinsa sun ba da gudummawa sosai wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa da ci gaban zamantakewar al’umma. Wannan ne tunanin da’a na gargajiya.
Wannan tunanin da’a na da dajara sosai. Ya zuwa yanzu yana da ma’ana kwarai. Darajarsa ta riga ta samu amincewar mafi mutanen duniya, tare da taka muhimmiyar rawa a ci gaban al’adun bil’adam.
Nuna biyayya da ladabi ga iyaye da bin umurninsu
Mutanen Sin su kan dauki nauyin dake kansu na kula da iyayensu. Sun yi imani cewa, duk wadanda suka nuna biyayya da ladabi ga iyayensu da ba da kulawa yadda ya kamata, suna iya bin hanyar gaskiya da amintacce a yayin mu’amala da sauran mutane. An samu labaru dangane da nuna biyayya da ladabi ga iyaye da yawa a gargajiyar kasar Sin, kamar “Dandana magani da kansa”, da “Ajiye Lemo a riga domin baiwa mahaifiya” da dai sauransu.
Labarin “Dandana magani da kansa” na nufin sarkin Wen na daular Han mai suna Liu Heng, wanda ya shahara sosai a sakamakon nuna biyayya da ladabi ga iyaye. Yayin da mahaifiyarsa take rashin lafiya na tsawon shekaru uku, Liu Heng ya kan zama tare da ita a maimakon yin barci. Duk magungunan da mahaifiyarsa za ta sha, shi da kansa ya kan dandana. A cikin shekaru 24 da Liu Heng ya rike da mulkin kasa, ya dora muhimmanci sosai kan kula da kasa bisa da’a, da raya ladabi, da bunkasa aikin gona, a kokarin tabbatar da dorewar zamantakewar al’umma, da samun ci gaba da farfadowar tattalin arziki yadda ya kamata. An dauki wa’adin aikinsa a matsayin sarkin kasa da na sarkin Jing na daular Han a matsayin kasa mai albarka mai lakabin Wenjingzhizhi.
Labarin “Ajiye lemo a riga domin baiwa mahaifiya” na nufin Lu Jin, wanda aka haife shi a yayin daular Sanguo. Yayin da shekarunsa ya kai 6 a duniya, Lu Ji ya kai ziyara a gidan Yuanshu dake yankin Jiujiang tare da mahaifinsa mai suna Lu Kang. Yuan Shu ya ba su lemo, sai Lu Ji ya ajiye guda biyu a cikin rigarsa. Yayin da suke yin ban kwana, lemo ya fada a kasa. Yuan Shu ya yi dariya da cewa, “Ka yi bakunci a gidana, ka ajiye lemo a buye, wannan ya yi daidai ne?” Lu Ji ya amsa cewa, “Sabo da mamana tana son cin lemo sosai, shi ya sa ina so na ba ta, domin ta dandana.” Da zarar Yuan Shu ya ji haka, ya ji mamaki kwarai da gaske.
Ko da yake a tsara mafi yawan labaran, amma mutanen Sin sun gaji da’ar nuna ladabi da biyayya ga iyaye yadda ya kamata.
A yayin daular Han, gwamnatin ta taba ba da umurni har sau da dama, domin sa kaimi ga nuna biyayya da ladabi da girmamawa tsofaffi. A daidai wannan lokaci, gwamnatin ta baiwa tsofaffin da shekarunsu suka kai sama da 70 a duniya kyautar wani irin kwajiri. Duk wadanda suke amfani da wannan kwajiri, suna iya samun kulawa ta musamman a zamantakewar al’umma. Bayan haka, a yayin daular Qing, sarakuna Kangxi da Qianlong sun gudanar da gagaruman bukukuwan girmamawa tsofaffi. Sarakuna biyu sun gayyaci tsofaffin da shekarunsu suka kai sama da 65 da haihuwa zuwa fadar sarki, wadanda yawansu ya kai sama da dubu daya a kowane lokaci.
Mutanen Sin su kan ba da kulawa ga ‘ya’yansu, tare da horar da su, cike suke da alhaki. Littattafan Jiezishu, da Jiaxun da dai sauransu da yawa da aka gada daga zamanin da, na kunshe da muhimmin ilmin koyar da ‘ya’ya, wadanda suke da daraja sosai da sosai a fannin da’a.
A yanzu an gaji al’adun nuna biyayya da ladabi da girmamawa ga tsofaffi da kula da yara. Tsofaffin Sin suna da ranar tsofaffi, yayin da yaran kasar suke da ranar yara bisa dokoki. Bayan haka, gwamnatin kasar Sin ta tsara dokar musamman domin kiyaye ikon mata da yara. Bugu da kari, a cikin dokoki an tanadi cewa, dole ne mazaunan kasar Sin su kula da iyaye da yaransu.
Wannan da’a ta tabbatar da dorewar iyalai da zamantakewar al’umma, kuma ta aza tubali ga samun bunkasuwar al’ummar kasar Sin yadda ya kamata.
Abokai uku na itacen Pine da gora da furannin Dinya
Mutanen Sin suna son itacen Pine da gora da furannin dinya cikin dogon lokaci, sabo da dukkansu sun yi kuzari a yanayin sanyi, kamar abokan arziki uku suke maraba da zuwan yanayin bazara. A sakamakon haka, an kira su “Abokan arziki uku a yanayin sanyi”, wadanda suka zama alamar da’a da mutanen Sin suke neman samu.
A kasar Sin, a kan samu zane-zanen “Abokan arziki uku a yanayin sanyi” a ko ina, kamar kayayyaki da tufafi da gine-gine da dai sauransu. jarumai suna sonsu a sakamakon da’arsu ta gwagwarmaya, yayin da farar hula ke sonsu a sakamakon rayuwarsu masu tsawo sosai da kuzari.
Itacen Pine na da karfi sosai wajen rayuwa, yana da launin kore ko a yanayin zafi mai tsanani. A sabili da haka, an ba su kyakkyawar da’ar taurin kai. A kasar Sin, mutane suna sonsu kwarai a sakamakon rayuwarsu a duk yanayi hudu na kowace shekara, har sun zama wakilan rayuwa masu tsawo sosai.
Duk lokacin da yanayin zafi ya zo, tsire-tsire da yawa su kan mutu. Amma gora ta kan ci nasara, ta tsaya a kankara da iska. Babu kome a cikin cibiyar gora, kuma ya kan tsaya yadda ya kamata. Shi ya sa a kan mayar da ita da’ar karbar shawara daga saura. Kuma a kan kira shi mai kirki. Bisa al’adun gargajiyar kasar Sin, a kan yi maraba da zuwan sabuwar shekara ta hanyar wasan wuta, a kokarin samun tsaro a shekara mai zuwa. A sabili da haka, gora ta zama alamar tabbatar da tsaro da samun alheri a kasar Sin.
Furannin dinya na shahara sosai bisa al’adun gargajiyar kasar Sin, wadanda suke da dadin ji. Furannin dinya sun sa kaimi ga jama’a da su samu ci gaba ba tare da kasala ba bisa da’arsu mai tsabta ta taurin kai da karbar shawarwari daga saura. A sakamakon haka, masu ilmi na dauloli daban daban sun rubutu wakokin yabawa furannin masu dimbin yawa. A kasar Sin kuma, a kan dauke su a matsayin wakilan zuwan yanayin bazara da samun fatan alheri. Tatsuniyoyi dangane da furannin dinya da ma’anarsu sun yadu sosai a Sin, tare da samun amfani.
Ban da “Abokan arziki na yanayin sanyi”, an samu tsire-tsire da yawa a kasar Sin, kamar furannin Chrysanthemum, da na Orchid, da na Lotus da dai sauransu, wadanda kuma aka samar da su kyakkyawar da’a. Sun zama alamar kyakkyawar da’a da mutanen Sin suke bi.