Haruna Akarada">

Nagoda Ya Koka Da Rashin Taimaka Wa Masu Hakar Kabari A Kano

Halin da makabartu su ka shiga, musamman na al’ummar Musulmi da ke a rewacin Nijeriya, inda babu wata makabarta da za ka shiga ka ga babu wani abu da ya kamata al’umma su gyara tun daga masu hakar izuwa masu kula da makabartar, abin takaici ne.

Wannan ya sa wasu daga cikin masu kula da makabartar dandolo da ke daf da kofar Kabuga a birnin Kano su ka mika kuka a gidan rediyo sakamakon alawus din da a ke ba su watanni da dama babu labari.
Jin wannan kukan nasu ya sa tsohon Mai Taimaka Wa Gwamna Kan Harkokin Makabartu, Alhajiji Nagoda, ya kai kukansu ga jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda ya shaida wa LEADERSHIP A YAU lokacin da ya ke mika wasu kudi kimanin Naira 50,000, ya ce, hankalinsa yanzu ya kwanta.
Ya ce, “wannan abin takaici ne, yakamata masu mulki su ji tsoran Allah. Dalili shi ne, duk mukaminka; ko gwamna ka ke ko shugaban kasa ka ke ko minista ka ke, wata rana a na iya tsintar ka a wannan guri, wato makabarta. Wannan ya sa mu ka yi magana da jagoranmu, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, domin taimaka wa wannan jama’a. Nan da nan ya bada umarnin cewa, duk makabartar da ke Jihar Kano a ba su Naira 50,000.”
Ya kara da cewa, “abin takaici ne a kasa taimaka wa masu hakar kabari da masu gadi. Duk wanda a ka ce ya zo ya zauna ya ke yin hakar kabari, an hada shi da aiki, amma wannan bayin Allah, nan su ke kwana su wuni, amma a ka kasa kulawa da su. Gaskiya wannnan abin takaici ne.”
Ya ce, “wannan tallafi da a ka kawo karkashin wannan tawaga ta Kwankwasiyya, domin taimaka wa wadannan bayin Allah, ya zama dole, domin sun hakura da komai sun dawo makabarta. Don me ba a taimaka mu su? Su nan ba sa tsoron maciji ko wani abu mai firgitarwa.”
Daga Sai ya yi kira da gwamnati da a yi gaggawar ba su hakkinsu. A karshe ya yi kira da masu dama da su kai tallafin izuwa makabartar da ke kusa da su, domin tallafa wa masu hidima ga makabarta, domin su na bukatar taimako sosai daga al’umma.

Exit mobile version