Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ƙaddamar da kwamitin mutane 10 da za su kula da harkokin alhazan Nijeriya a dandalin sadarwar Saudiyya, Nusuk Masar, a shirye-shiryen Aikin Hajjin 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Hukumar kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ahmad Mu’azu, ya fitar a ranar Juma’a, 14 ga Nuwamba 2025. Ƙaddamarwar, wadda aka gudanar a ofishin NAHCON da ke Makka, na daga cikin muhimman matakan farko na shirin Hajjin shekara mai zuwa.
- Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
- ‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026
Dandalin Nusuk Masar, karkashin Ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya, shi ne babban dandali da ke ɗauke da muhimman ayyukan Hajji, ciki har da rajistar maniyyata da biza da masauki da abinci da hidimomin Mashair da kuma tsarin bayanan tashi da saukar jirage. Sabon kwamitin da aka ƙaddamar zai jagoranci duk al’amuran da suka shafi Nijeriya a waɗannan muhimman bangarori.
A jawabinsa, Farfesa Usman ya bayyana aikin kwamitin a matsayin wani da zai taka muhimmiyar rawa da ɗaukar alhakin da “ya ta’allaka da ingantaccen gudanar da hidimar alhazan Nijeriya a Hajjin 2026,” yana mai jaddada cewa ana sa ran kwamitin zai tabbatar da inganci, gaskiya, da isar da rahotanni a kan lokaci a dukkan matakai.
Ya ce jin daɗin kowane ɗan Nijeriya a Hajjin 2026 zai dogara sosai kan yadda kwamitin zai gudanar da aikinsa, yana mai bayyana cewa rawar da ake takawa a dandalin Nusuk Masar ta yi daidai da rawar da jiragen sama da sauran masu ba da hidimomin Hajji ke takawa.
A nasa jawabin, Kwamishinan PPMF, Prince Aliyu Abdulrazaq, ya shawarci kwamitin da su gudanar da aikinsu da amana, gaskiya, da ƙwarewa, yana mai cewa dole ne amincewar da Hukumar ta yi musu ta bayyana a sakamakon aikinsu.
Da yake magana a madadin kwamitin, Jagoran Kwamitin, Dr. Haruna Danbaba, ya tabbatar wa Hukumar cewa za su bi dukkann ka’idojin da Ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa, tare da tabbatar da cewa ba’a samu jinkirin wajen gudanar da aikin kwamitin ba.
Ƙaddamar da kwamitin na daga cikin manyan matakai na farkon shirin NAHCON domin Hajjin 2026, kuma ana sa ran fara aiwatar da muhimman ayyuka nan take.














