Nahiyar Afrika Ba Dandalin Gasa Ne Tsakanin Manyan Kasashe Ba

Nahiyar Afrika

Daga CRI Hausa,

Mai taimakawa ministan harkokin wajen Sin, Wu Jianghao, Ya ce bai kamata nahiyar Afrika ta zama dandalin gasa tsakanin manyan kasashe ba, sai dai dandalin hadin gwiwar kasa da kasa.

Wu Jianghao ya bayyana yayin wani taron manema labarai da aka yi jiya a birnin Beijing cewa, taimakawa nahiyar Afrika, hakki ne na bai daya, da ya rataya a wuyan kasa da kasa.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da fatan ganin hadin gwiwar sauran kasashe da na nahiyar Afrika.

Da yake jaddada wannan batun, shugaban sashen kula da harkokin nahiyar Afrika na ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wu Peng, ya ce ya zama wajibi bukatun Afrika ya kasance jigo cikin hadin gwiwar Sin da Afrika da hadin gwiwar sauran kasashe da Afrika. (Fa’iza Mustapha)

 

 

Exit mobile version