A birnin Mombasa, mutanen da suka yi sammakon fita a ranar Laraba sun ga wani abin al’ajabi, bayan da suka ga wasu mazaje biyu tsirara suna laluben wata babar mota.
Jikin mutanen duk tabo kuma baya maciji ya kanannade wuyansa. Motar ta wata mata ce da tuni ta sanar da jami’an ‘yan sanda cewa an sace ta.
Wani boka da yayi ikirarin cewa shi ne ya yi tsafin da ya kama wabanda ake tuhuma da satar motar ya bukaci a biya shi dalar Amurka 1,000 kafin ya lalata tsafin.
Labarin ya ja hankulan mutane har wata tashar talabijin ta tafi wurin kuma ta nuna wa al’umma yadda lamarin ke gudana kai-tsaye.
‘Yan sanda sun kama duka mutanen su hudu, kuma sun gurfanar da su a gaban wata kotu.
Domin mallakar macijin, an tuhumi bokan da taka dokar da ke kare namun dawa a kasar ba tare da izini ba.
Kotun ta bayar da umarnin a duba lafiyar wadannan mazan guda biyu da aka same su tsirara, kuma ita matar an tuhume ta da sanar da ‘yan sanda labarin boge.