Rabiu Ali Indabawa" />

Naira 10,000 Ta Sa Jami’ar ABU Ta Kori AB Umar Ba Neman Daliba Ba

Wasu sabbin rahotanni da su ka fito ba da jimawa ba na nuni da cewa, Naira 10,000 ne su ka yi sanadiyyar da AB Umar ya bar aiki a jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya shekarun baya da su ka wuce.

Yanzu haka dai jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da AB Umar daga aiki bisa zargin cewa ya na neman dalibansa ’yan mata. Daily Trust ta bi diddigin labarin wannan malamin jami’a, inda ta samu labari cewa, tun farko an sallami malamin makarantar daga aiki ne a Jami’ar ABU Zariya, inda ya baro saboda ya karbi kudi Naira dubu 10 wajen daliba. A dalilin wannan ya rasa aikinsa.

“Abin da ya faru shi ne ya nemi 10,000 daga hannun wata dalibarsa, ita kuma ta yarda za ta ba shi, amma da bukatar ya ba ta lambar asusunsa. Daga nan sai ta aika kudin zuwa bankinsa.

“Ita kuma wannan daliba sai ta yi amfani da takardar da ta tura kudin, ta rubuta wasika zuwa ga shugaban jami’ar lokacin, Farfesa Abdullahi Mustapha, cewa malami ya bukaci kudi a hannunta.

“Daga nan shugaban jami’ar ya nemi shugaban jami’an tsaron ya binciki lamarin. CSO ya kafa kwamitin bincike, amma a ka gaza samun hujjar da ke nuna dalilin da ya sa a ka ba da kudin.”

“Abin da a ka gagara ganewa shi ne ko shin kyauta a ka ba wa malamin ko kuma tursasa dalibar ya yi,” in ji majiyar, ta na mai cewa, “Umar ya fada wa wannan kwamiti cewa, ya roki kudin ne saboda Iyalinsa sun shiga wani hali.

“Malamin ya kare kansa da cewa ba matsa wa dalibar ya yi ba, domin bai yi ma ta alkawarin komai ba. Duk da haka kwamitin sun ga laifin Umar, amma babu wanda ta jefe shi da zargin yunkurin lalata da ita.”

Majiyar ta ce, a karshe sai dai a ka bukaci a kawo karshen aikin Umar a sashen koyar da aikin jarida (ba bangaren Ingilishi da a ke fada ba), amma a lokacin ba a same shi da laifin yin lalata ba.

Exit mobile version