Connect with us

NOMA

Naira Biliyan 102 A Fannin Noman Nijeriya Za Su Taimaka – NIRSAL  

Published

on

Kamfanin bunkasa dubarun aikin gona na Nijeriya NIRSAL, ya ce ya samar da naira biliyan 102 a shekaru hudu da suka wuce, da zai zuba a bangaren ci gaban kasuwancin noma.

Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da ’yan jarida a Abuja.

A cewar Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed, an tattara kudaden ne daga farkon kafa kamfanin, ba tare da tallafin gwamnati ko babban bankin Nijeriya ba.

Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed, ya ce da wannan ci gaba da kamfanin ya samu, gwamnatin tarayya na da damar bunkasa bangaren da za ta ci moriyar sa.

A wani labarin kuma, kamfanin na NIRSAL, ya kulla wata yarjejeniya da kamfanin Microsoft domin samar da manhajar Azure FarmBeats da za ta taimakawa manoman Nijeriya wajen samar da amfanin gona, rage kashe kudade tare da bunkasar bangaren.

Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed, ya ce kamfanin ya zabi manhajar ne saboda za ta fi dacewa bin diddigin harkar noman kasar, wanda wani babban bangare ne da ke taimakawa kamfanin wajen samar da kudaden noma da zuba jari.

Ita dai wannan manhaja ta Azure FarmBeats, na taimakawa wajen tattara bayanan aikin gona, bada hasashen lafiya da yanayin kasar gona, bayanan tsirrai da yawan gonakai ta hanyar yin amfani da hanyoyin tattara bayanai na zamani.

A wata sabuwa kuwa kungiyar masu masana’antu ta kasa ere- MAN ta sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sake bude iyakokin kasar nan na kan tudu data bayar da umarnin a garkame su.

Shugaban sashen bunkasa fitar da kayayyaki na kungiyar Ede Dafinone ya yi wannan kira a wajen wani taron karawa juna sani da hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta shirya a Lagos.

Ya ce yan kungiyar sun zauna da gwamnati kuma sun fahimci kokarin ta na magance matsalar shigo da haramtattun kayayyaki a kasar, amma dai duk da haka akwai butatar bada dama ga sahihan yan kasuwa da ke bukatar yin kasuwancin su da kasashe makwabta.

Dangane da taron karawa juna sanin, da kuma kaddamar da cibiyar kyautata kasuwanci, da cinikayyar intanet na majalisar dinkin duniya, Dafinone ya ce saukin isar da kaya ga abokan hudda a yankin yammacin Afrika harma turai da yankin Amirka ya ta’allaka ne ga irin saukin shige-da-fice da masu safarar kayan suka samu.

Da ya ke tsokaci kan kare tattalin arzikin kasar, Dafinone ya ce gwamnati na yin dukkan mai yiwuwa wajen saukaka kasuwancin shige-da-ficen kayayyaki da musamman don taimakawa kasar fadada hanyoyin tattalin arziki daga man fetur.

A cewar Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed, an tattara kudaden ne daga farkon kafa kamfanin, ba tare da tallafin gwamnati ko babban bankin Nijeriya ba.

Manajan Daraktan kamfanin Aliyu Abdulhameed, ya ce da wannan ci gaba da kamfanin ya samu, gwamnatin tarayya na da damar bunkasa bangaren da za ta ci moriyarsa.
Advertisement

labarai