Connect with us

KASUWANCI

Naira Biliyan 65 Aka Zuba A Kasuwar Hannun Jari A Wannan Zangon

Published

on

A bisa yadda masu fashin bakin suka sa rai kasuwar shinku ta kasa a lokacin da kasuwar taci a ranar talatar data gabata,  wasu kamfanonin da suka fadi warwas a kasuwar suka samu farfadowa har suka samu ribar data kai ta naira biliyan 65 a kasuwar a karashen hada-hadar da akayi a kasuwar. Kamfanin FBN Holdings Plc ya samu kashi  6.71 bisa dari, Nestlé Nigeria Plc nada kashi  2.26 bisa dari, United Bank for Africa Plc nada kashi  6.94 bisa dari, inda kasuwar ta kai tanada  naira tiriliyan 11.821 daga naira tiriliyan 11.756 a ranar litin data gabata. Jimlar kaya miliyan 269.814 da aka kiyasta sun kai yawan naira biliyan 2.653 da aka yiu ahada-hadar su a kasuwar a cikin kaya 4,705 inda kamfanin First Aluminium Nigeria Plc yake da 27 dukkan kuma shiyar ta kai samada da 56 samada to 32,381.00 bps. Har ya zuwa yau, an samu kari ya kai kashi 15.3 bisa dari, inda kuma ayyuka suka kara karuwa da kashi 23.3 bisa dari, sai kashi 67.9 bisa dari inda suka kai naira biliyna  2.653 da naira miliyan  269.814. Manyan kayan dake a kan gaba da akayi hada-hadarsu a kasuwar sune bankin Access Bank Plc yake danaira miliyan N679.8, Zenith Bank Plc naira miliyan N338.4, International Breweries Plc nada  naira miliyan  N229.7, inda a cikin su Bankin Access ne ke a kan gaba da naira miliyan  84.9,  sai Bankin Skye Plc nada naira miliyan 22.9 sai Bnakin Zenith nada naira miliyan16.4. Bankin Zenith da UBA sun samu karin kashi 1.26 bisa dari, inda kuma na sarrafa mai da iskar gas ya haura zuwa kashi 0.32 bisa dari na ribar kudin ruwa da kamfanin Forte Oil Plc, Eterna Plc, Nestle da  kamfanin Dangote dake sarrafa Sikari. Na masana’anta ya kai zuwa kashi 0.02 bisa dari na farashin kamfanin Cutid Plc. A bangaren na inshora kuwa an samu asara data jai ta kashi 0.25 bisa dari   bayan da kamfanin inshora na Unibersal Insurance Plc da  Cornerstone Insurance Plc suka auka cikin wani yanayi. Biyar dakke a kan gaba da suka tabka asara sune  First Aluminium Nigeria Plc, Prestige Assurance Plc, Royal Edchange Plc, Unity Bank Plc, Union Diagnostic da kuma Clinical Serbices Plc.  Kamfanin First Aluminium shiya dinsa ta karu zuwa kashi 10 bisa dari aka kuma rufe a kan 0.33, sai kuma kamfanin inshora  na Prestige Assurance da farashin ya ya yi kasa da kashi 9.62 bisa dari aka rufe a kan  a kan shiya57. Bankin Royal Edchange, Unity Bank, da kuma  Union Diagnostic sun raba shiya data karu zuwa kashi  9.52  bisa dari, da kashi 9.41 biusa dari 9.38 aka kulle a kan  naira 0.23, naira0.93 da kuma naira  0.35.Kamfanoni biyar na Red Star Edpress Plc, Standard Alliance Insurance Plc, Cornerstone Insurance Plc, Sobereign Trust Insurance Plc da kuma na  Unibersal Insurance Plc. Dukkan su sun durkushe da kashi 9.09 bisa dari, 8.70  da kashi  8.70 da kashi  8.33  bisa dari da kuma kashi takwas bisa dari baki daya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: