- Za Ta Iya Kai Wa Dala 500 Cikin Mako Mai Zuwa
Daga Mahdi M. Muhammad,
Hukumar Kula da Dillancin Kasuwannin Kudi a Nijeriya (FMDQ) ta bayyana cewa, duk da hauhawar farashin danyen mai a wannan makon, dorewar bukatar Dala a kasuwar canjin kudade na waje yana nufin kudin Nijeriya na iya hawa a karshen mako da kashi 0.18 cikin rauni.
Bayanai daga hukumar ya nuna cewa, cinikin kudin waje a hukumance ya nuna cewa, an yi musayar Naira da Dala akan Naira 411, idan aka kwatanta da Naira 409.20 da aka rufe a ranar Litinin 1 ga Maris, 2021.
Darajar canjin ranar Juma’a kuma tana wakiltar Naira 4.5 ko 1.10 cikin 100 na faduwar darajar daga Naira 406.50 a ranar Alhamis 4 ga Maris. A zahiri, a ranar Juma’a, darajar Naira ta yi sama a farashin da yakai N415 a Dala daya.
A kasuwar da ba ta hukuma ba, bayanai sun nuna cewa, kudin cikin gida ba su canjawa a Dala 480/1 a cikin mako, amma yana iya canjawa a mako mai zuwa.
Canje-canjen na ‘Fored’ a hannun jari da masu fitar da kaya (I&E) duk da haka ya karu da kashi 25.29 bisa dari, tare da dala miliyan 83.93 da aka rubuta ranar Juma’a sabanin dala miliyan 66.99 da aka saka ranar Alhamis.
Rahotanni a shafin yanar gizo na CBN ya nuna cewa asusun ajiyar Nijeriya na waje, wanda ya baiwa babban bankin kasar tsokar kare Naira, ya ragu da dala miliyan 184.5 zuwa dala biliyan 34.91 kamar yadda yake a ranar 3 ga Maris, 2021, idan aka kwatanta da dala biliyan 35.09 kamar yadda yake a ranar 26 ga Fabrairu, 2021, lokacin an rage darajar Naira.
A cikin Fabrairu 1 zuwa 26 kadai an samu raguwar ajiyar waje ya kusan dala Biliyan 1.1. Ragowar adadin ya nuna cewa, CBN na yin duk abin da zai iya don biyan bukatar karin dala daga masana’antu da ‘yan kasuwa don nisanta su da kasuwar da ke daidai da kuma dakatar da sayayyar musayar kudaden waje.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, a kwanan baya ya jaddada bukatar da ke akwai na hana babbar raguwar ajiyar waje ta hanyar inganta samar da kayayyakin da ake shigo da su cikin gida.
Amma ya lura cewa kasar tana da isassun kudaden da zata dauki nauyin watanni bakwai masu zuwa na shigo da kayayyaki kuma ba bukatar firgita.