Da ya ke jawabi a madadin hukumar UNICEF a Nijeriya Mista Peter Hawkin ya ce; Sakamakon halin rashin ingantaccen ilimin zamani da yara ba su mora. Majalisar Dinkin Duniya za su hada hannu da kungiyar UNICEF wajen farfado da ilimin yara kanana a Najeriya.
Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF ta bayyana matukar takaicin ta wajen yadda Najeriya ta zama koma baya a kan abin da ya shafi ilimin yara.
Sun kara da cewa, “Najeriya ita ce take da adadin yara wanda adadin su ya kai kimanin Milyan 10.5, wanda ba sa zuwa makaranta.
Ta ce; za su yi iya mai yiwuwa wajen tsara yadda yara za su dinga samun zuwa makaranta a taron da za a yi na ranar ‘yancin yara ta Duniya karo na 30 na wannan shekaran, domin Yaran su ne matasan gobe.
Saboda daukaka da samun duk wani matsayi yana samuwa ne ta bangaren ilimi. Kasa ba ta ci gaba matukar yaran su ba su da ilimi. Masu ilimi su ke gina kasa da bunkasa tattalin arzikin kasar.
Babu wata kasa da take barin yaranta masu tasowa babu tunanin me za mu bunkasa domin ci gaban kasarmu.
Ta ce; wannan kalubale ne ga mahukuntan Nijeriya kuma idan wadannan yaran ba su samun karatu to nan gaba me ake bukatar su zama? Kenan nan gaba ba za a samu ingantattun Ma’aikata ba. Haka ma kereikere ba zai yawaita ba.