Connect with us

WASANNI

Najeriya Mu Ke So A Gasar Cin Kofin Duniya, Cewa Kungiyar Roma

Published

on

 

Kungiyar kwallon kafa ta AS Roma ta kasar Italiya ta ce za ta goyi bayan ‘yan wasan Super Eagles a Gasar Cin Kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni mai zuwa.

Kasar Italiya tana daya daga cikin kasashen da ba za su je gasar ba ta bana wadda za a yi a kasar Rasha saboda basu samu damar zuwa ba kuma wannan ne karo na farko da za’a buga gasar babu Italiya kusan shekaru 60 da suka gabata.

Sai dai Najeriya tana cikin kasashen nahiyar Afirka biyar da suka samu gurbin zuwa gasar kuma Super Eagles din ta fito a rukunin daya hada da kasar Argentina da Iceland da kuma kasar Crotia

Kungiyar AS Roma ta bayyana a shafinta na sada zumunta (Tiwita) cewa za ta goya wa ‘yan wasan Najeriya baya a lokacin gasar.

Akwai dan Najeriya Sadik Umar wanda yake taka leda a kungiyar Roma kodayake yanzu haka an ba da shi aro a kungiyar NAC Breda a kasar Netherlands.

Masu sharhi kan wasanni suna ganin matakin kungiyar zai kara mata farin jini a idon ‘yan Najeriya.

Najeriya tana rukunin D ne a gasar wanda ya kunshi kasashen Croatia da Iceland da kuma Argentina.

 
Advertisement

labarai