Jiya ranar 27 ga wata, an kaddamar da cibiyar horo ta Luban ta kasar Sin a Najeriya, da nufin ba da horon dabarun fasaha domin taimakawa daliban kwaleji cimma bukatun kasuwa. Cibiyar wadda jami’ar Abuja ta karbi bakuncinta, za ta fara ne a matakin farko da kwasa-kwasan da suka hada da kula da zirga-zirgar jiragen kasa da gadoji da ramukan jiragen kasa.
Wannan cibiyar horo ta Luban yana daya daga cikin cibiyoyin horo na Luban guda goma da kasar Sin ta shirya kafa su a kasashen Afirka a karkashin inuwar dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka ta FOCAC, wanda ta sanar a watan Satumban shekarar 2018, a kokarin koyarwa matasan Afirka fasahohin sana’o’i.
Dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka ta FOCAC da aka kafa a shekarar 2000 wani muhimmin dandali ne da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka guda 54 wajen hadin gwiwarsu ta a zo a gani, kana wani sabon tsari ne da ya martaba ka’idar kasancewar bangarori daban daban da ma hadin kan kasa da kasa. A cikin shekaru 20 da suka gabata, Sin na bin dabarar “cimma muradu da kuma martaba ka’idoji” da ma dukufa wajen hadin kan bangarorin biyu don samun nasara da bunkasuwa tare.
Sakamakon da aka samu a karkashin inuwar FOCAC ya amfani kasashen Afirka daban daban. Alal misali, Tarayyar Najeriya ta ci gajiyar dandalin FOCAC sosai. A cikin wadannan shekarun baya, Najeriya ita ce wadda ta fi samun yawan kwangilolin gini da samun kayayyakin kasar Sin a nahiyar Afirka, kana ta zama abokiyar cinikayyar Sin mafi girma ta biyu a Afirka. A shekarar 2019, jimillar cinikayya a tsakanin Sin da Najeriya ta zarce dala biliyan 19.2, wadda ta karu da kaso 26.3 bisa ta shekarar 2018, saurin karuwar jimillar ya zama na farko a cikin muhimman abokan cinikayyar Sin guda 40. Bugu da kari kuma, hanyoyin dogo a tsakanin Abuja zuwa Kaduna da tsakanin Lagos zuwa Ibadan da cikin Abuja, tashar samar da wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa ta Zungeru, tashar jiragen ruwa ta Lekki, yankin cinikayya marasa shinge ta Guangdong da ke Ogun, yankin ciniki cikin ’yanci na Lekki da kasar Sin ta gina sun aza harsashi mai inganci ga ci gaban masana’antun Najeriya. Ban da wannan kuma, cudanyar al’adu a tsakanin bangarorin biyu ta kara bunkasuwa, inda yawan daliban Najeriya da ke karatu a kasar Sin ya kai 6800 a shekarar bara, adadin da ya zama na farko a Afirka.
Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, an samu sakamakon a zo a gani a karkashin inuwar FOCAC, wanda ya kawo wa jama’ar Sin da Afirka alheri sosai. Hadin kai a tsakanin bangarorin biyu ya taimaka wa farfadowar al’ummar Sin, yayin da ya kara azama ga ci gaban Afirka bisa karfin kansu. Lamarin kuwa ya shaida cewa, kasashe masu tasowa na iya samun wata hanyar farfardowa da ta dace da yanayinsu bisa karfin da suke da shi. (Marubuciya: Kande Gao)