Connect with us

TATTAUNAWA

Najeriya Ta Fita Daga Kangin Mulkin Mallaka Ta Fada Na ’Yan Boko – Sani Brothers

Published

on

ALHAJI SANI YUNUSA SARINA, wanda a ka fi sani da ALHAJI SANI BROTHERS, na daya daga cikin dattawan Arewa da ke zaune a Kano, wanda ya haura shekara 70 a duniya, ya na daga cikin masu kishin ganin al’umma da ganin kasa sun gyaru. Don haka ya kasance mai bin diddigin al’amuran yau da kullum da kuma bada shawarwari da fadakarwa da fadakar da al’umma da shugabanni a Nijeriya, inda a wannan hira ya tabo al’amuran tattalin arziki, noma, tsaro, sufuri da dai sauransu, inda kuma ya tabo keta da babakere na wasu daga cikin masu ilimin boko marasa kishin kasa da dai sauran abubuwa muhimmai a Nijeriya a cikin hirarsa da ’yan jarida a Kano, wanda Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUSTAPHA IBRAHIM, na daga cikin ’yan jaridun. Ga yadda hirar ta kasance:

Da farko dai ranka ya dade za mu so mu ji wacce shawara za ka ba al’umma da shugabanni bayan bude gari da aka yi bayan kulle a sakamakon Korona?
To ba shakka an bude gari bayan kulle da muka sha na tsawon mako shida a nan Kano kuma duk dai abinda ya faru, ya faru ne sakamakon zuwan wannan cuta ta annobar Korona wanda shugabanni suka ga abinda ya da ce su yi kenan domin yakar wannan cuta ta Korona to kuma gashi yanzu a iya cewa mu dai anan Kano Alhamdulillah an samu saukin ta sakamakon addu’o’i da kuma matankan da shi Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dauka akan wannan cuta ta Korona.
To kuma ita kasan gwamnati ita ce kusan abinda ya dace tayi a duk lokacin da wani abu ya zo domin sau da yawa zaka ga idan hukuma tayi abu sai a ga kamar bai dace ba, amma kuma ita hukuma ita ta san meye dalilin da yasa ta dau wannan mataki to kuma dama kullum idan abu ya faru hukuma ta dau mataki wani zai yi masa dadi, wani kuma bazaiyi masa dadi ba dama haka abu yake wani fahimta wani kuma bai fahimta ba to mu dai addu’ar mu Allah ya kare mu daga dukkan wani abun ki ya bamu lafiya da zaman lafiya a Kano da ma Najeriya da duniya baki daya.
Haka kuma Nasiha ko shawara ga shugabanni shi ne cewa aji tsoron Allah duk abin da za’ayi ayi dogon tunani akansa a tuna cewa a wannan rayuwa akwai mai karfi, akwai kuma marasa karfi ka ga mu anan Kano za kaga mutane kashi 80 cikin 100 sai sun fita zasu sami abinci to ka ga dole a lura da wannan  domin ko mutum musulmi ne ko ba musulmi ba idan yana da addini to ya san ranar alkiyama za’a tambayeshi dukkan abinda ya yi na dai dai ne ko na akasin haka, dan haka ka da a manta da wannan rana na zuwa sai dai kawai Allah ya yi mana gamdakatar amma dai kowa ya san za’a tambayeshi abinda ya aikata domin shi kansa mulki jarabawa ce kuma adalci da tausayi wajibi ne akan kowa, kuma ita al’umma musamman talakawa da ake karkashin shugabanni su kasance masu sanin abinda ya kamata a ko yaushe ta hanyar jin tsoron Allah da kyakkyawan mu’amala ta gari.

Alhaji, ka na cikin dattawa manoma kuma dan kasuwa banda kasancewar ka mai kamfanin zirga-zirga fittace a kasar nan me zaka ce dangane da karancin taki da manoma musamman kanana ke kuka da karancinsa a yanzu?
Wannan Magana ce mai fadi sai dai a takaita ta yanzu dai kasan muna watan bakwai wanda ke nuna cewa damuna tayi nisa sosai kuma ba taki kamar yadda ka fada yanzu a wannan tambaya, To abinda zance shi ne mun fita daga kangin  yan mulkin mallaka Turawa mun shiga kangin mulkin mallakar yan boko wadanda duk su ne masu hargitsa abu da lalata abu saboda san zuciya na wasu yan bokon da muke da su idan Gwamnatin Tarayya ko ta Jiha zata bada wani tallafi musamman na Noma da muke magana yanzu su wadannan yan bokon sai suje su kama gonaki su karbe tallafin duk wani abu da ka sani da ance ga tallafi su ne kan gaba suje suyi ruwa suyi tsaki komai su karbe da sunan sune wadannan manoman ko wani abu mai kama da wani abu, wannan idan wani bai san haka ba, wasu sun sani kuma alhamdulillahi nima na san haka. Haka kuma za ka ga su ne Manoma, su ne masu harkar sufuri, su ne yan kwangila su ne yan kasuwa su ne komai sun kware wajan shan kai da tare abu alkairi kar ya zo kan talakawa wadanda aka yi dan su, saboda haka shi ne ya sa ake samun matsala a komai da gwamnati ke san taimakawa al’umma a koda yaushe, kuma wani abun mamaki shi ne wadannan yan boko masu rike da mukaman gwamnati kashi 80 cikin 100 ya’yan talakawa ne, amma kujerar mulki ya sa sun manta da halin da talakawa ke ciki na a taimaka mu su, saboda haka sai gwamnati ta dau mataki na ba sani ba sabo wajen takawa wasu yan Bokon marasa tausayi birki wanda suka fi turawan mulkin mallaka azabtarwa da rashin sassauci a zukatan su domin turawa su na da sassauci akan wasu yan bokon sannan za’a daina samun irin wannan matsala ta taki da ma sauran matsaloli da suka addabi al’ummar mu ta yau.

Ranka ya dade wasu na da ra’ayin cewa wannan karancin taki ya samo asali ne sakamakon lalacewar wani kamfani a fatakwal dake ba da sinadarin hada taki da kuma gazawar kwamitin da shugaban kasa ya kafa na samar da taki?
Koma dai me ya faru wannan abu sunan shi sakaci domin akwai abinda ake cewa gidan biyu maganin gobara, harkar noma harka ce da wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bawa muhimmanci dan haka wajibi ne duk wani abu da ya shafi noma ya zamana anyi tsari na daya da na biyu abinda bature yake cewa Plan A da Plan B wato idan na farko ya karye an dauko na biyu domin duk abu mai muhimmanci ba zaka yi mai sakwa-sakwa ba, kuma babu wani shugaban kasa da zai zo Najeriya ya ce yana san kasar ta cigaba kuma yayi wasa da harkar noma dan haka muhimmancin noma ya kamata a ce ba’a samu kowacce matsala da zata kawo koma baya a cikin sa ba saboda haka rashin yin aikin wani kamfani na samar da sinadaran taki da kuma gazawar kwamitin samar da taki na shugaban kasa da ake zargin kwamitin da gazawa ba zai zama uziri na karancin taki ba, ya kamata a dau mataki na samar da wadatattacen taki ga manoman mu na Najeriya domin samar da abinci wadatacce wanda ko a yanzu mun ga ranar noman nan wanda da ba’ayi Noma an samu wadataccen abinci a Najeriya ba, da Allah kadai yasan inda farashin shinkafa zai kai ko masara da dai sauran kayan abinci musamman a zamanin wannan Koronar  ba mamaki ace shinkafa ta kai dubu 50 amma saboda Allah ya bamu abinci, Allah ya takaita abun a haka, idan ka tuna masara da kaka ba ta kai dubu 10  amma kafin Azumi ya wuce, sai da ta kai dubu 20 tunda ta kai dubu 18.

Akwai shirin sa matasa a harkar noma kamar yadda ministan aikin gona ya yi bushara da hakan, yaya kake ganin wannan abu?
To Gaskiya wannan abu ne mai kyau sai dai akwai illoli ko matsaloli a cikin wannan shiri da za’a fuskanta, illa ta farko su matasan zasu yi? Shin an wayar musu da kai sun san muhimmancin Noma, za’a iya tursasa musu su yi? Domin yanzu abinda yak e faruwa shi ne da mutum ya yi Boko sai ya ga shi ya wuce ma yaje ya yi noma, sai dai ya shiga gwamnati ya kwashi dukiya ya gina gida a auri mata a siye mota shi ne burin dan Boko, a yayin da wata kasa a jiragen sama ana aiki da su wajen bunkasa noma a zamanance dama shi ilimin boko ilimi ne na sana’a da sabanta sana’o’i da aka gada, gadan gado kamar noma, kiwo, dinki, dukanci, fatauci, sufuri da dai sauran dukkanin sana’o’i  da suke taimakawa jama’a a rayuwa, ammafanin boko ka sabanta sub a kace ka wuce yin su ba. Kuma daman ai akwai ilimin zamani, ilimi ne na sana’a bai kamata ya zama na cima zaune ba inganta abinda ka gada musali ina da gona daya da na gada tun bani da aure, nayi aure na hayayyafa ai wannan bazata ishemu ba amma ta hanyar tallafin ilimi nawa da taimakon na hukuma  sai a samu mafita, shi kuma ilimin Addini ai ilimi ne da ke koyar da ibada da kyakkyawar mu’amala kasan haram kasan halak ka kuma zama mai hankali da sanin ya kamata da dai sauran duk wani abu na alkairi na cikin ilimin Addini kaga dole muyi amfani da kowanne ilimi wajen inganta rayuwar mu ta duniya da lahira.

Ko kana da wani abun cewa akan maganar ministan ayyuka na cewa ba da dadewa ba Niriya za ta iya samar da kwalta a cikin gida?
To ni a nawa ganin ya kamata ace Najeriya tuni ta wuce wanann matsayi domin duk wani abu da ake hada kwalta da makamantansu Allah ya bamu a Najeriya kamar Dutse, Kyakkyawar kasa, Yashi da dai makamantansu, to ya kamata ace tuni mun wuce wannan wajen, ni ina ganin ma kamar abin kunya ne ace muna da matsalar hanyoyi a kasar nan. Kuma su kansu hanyoyin ai akwai matsalar rashin bin ka’idojin hanya da muke fama da shi da rashin kayayyaki na kula da hanyoyi kamar yadda yake a da ana gwada duk motar da ta dauko kaya, idan ance wannan titi ko hanya data dau mota da kaya Ton 30 to a da ba za’a wuce haka ba amma yanzu sai a dau Ton 70 dole hanya ta lalace kuma idan ma an zo da wani tsari na kula da hanya sai kaga wadanda aka sa su kula da hanyar basu san hanyar ba, basu san tuki ba, basu damu da kishin rayukan mutane ba da dai sauran matsaloli da ke lalata hanyoyin mu wanda ake samun hatsari da rasa rayuka shi ma ya kamata a dawo da yanda abun yake ko kuma a zamanantar da shi ya fi na da wannan shi ne shawara ta.

A kusan karshe akwai maganar da ake yi yanzu ta mukaddashin shugaban hukumar EFCC Mustapha Ibrahim Magu ya ka kalli abu a matsayinka na daya daga cikin dattawan Arewa?
Maganar cin hanci, magana ce mai rikitarwa a Najeriya ni da ku yan jarida duk mun san wannan, maganar Magu magana ce da aka dade ana yinta, majalisar dattawa ta baya wacce su Bukola Saraki suka jagoranta taki amincewa da tsarkin Magu bisa dogaran ta da rahotan jami’an tsaron sirri akan Magu wanda hakan ya sa taki nadashi a matsayin shugaba aka ta dauki ba dadi tsakanin Majalisa da shugabannin zartarwa na gwamnati har aka zo dai wannan lokaci. To kaga abun akwai daure kai tunda jami’an tsaron nan a karkashin shugaban kasa suke to kuma har aka zo wannan karo na biyu wannan abu ya faru, to ana gayawa shugaban kasa kuwa komai kuwa kan wannan abu, to indai ya san wannan magana Ta rashin tsarkin Magu kuma har aka zo wannan yanayi to an samu matsala kenan akan yaki da cin hanci da rashawa ya samu koma baya kenan to sai mu ce Allah ya kawo karshen duk wata matsala da koma baya ga Najeriya.

A karshe meye shawarar ka yadda za’a samu cikakken tsaro a kasar nan musamman wasu da suke ganin sai anyi tankade da reraya ga shugabannin tsaron kasar nan me zaka ce?
To shugaban kasa dai tsohon Soja ne kuma har ya kai Janar kaga ba zaka ce komai ba kan harkar tsaro shi yasan yadda ya kamata ayi na samar da tsaro a kasa, Amma indai ana maganar harkar tsaro dai da kudi ne to sai ince masana tattalin arziki sun kasa a nan domin akwai hanyoyi masu sauki da za’a samu kudi mai yawa ta yadda zasu iya tafiya kai tsaye zuwa ga harkar tsaro misali ance ana fitar da mai da ake amfani da shi mai yawa a kullum wanda koda a ganga miliyan 40  ne ko lita ne ake amfani da shi ace duk lita a ware kudin harkar tsaro kwabo 50 miliyan nawa kenan a rana, ace kuma duk motar da ta bi hanya za’a biya naira 50 ko 100 na harajin tsaro kuma asa mutanen amintattu a harkar ba gara ba zago dan a samar da tsaro wannan harajin wa zai dama indai za’a samar da tsaron a kasa? Idan akayi la’akari da abubuwan da suke faruwa a yanzu ! amma sai ka rasa ina masana tattalin arzikin suke ina yan bokon suke? Da ba zasu bada wadannan shawarwari ba ko wadanda suka fi wannan. Wata babbar matsala ita ce kawai fa ana maganar takardar ka kamala makaranta kaza ne, ita ko takarda bata aiki sai dai suna gogayya da hangen nesa da basira sune suke aiki amma matsalar mu  duk basirar ba da gogewar ka a gurin yan boko idan baka da takardar karatu ka za, to kai baka san komai ba a gurin su, to su da suka sani suyi amfani da ilimin mana idan suna da shi a zahiri ba a takarda ba wajen warware matsalolin mu na Najeriya kodai sai kurin takarda kawai bamu ga aikin ta ba, wannan shi ne sakona kuma shi ne nake so a gane cewa amfanin ilimi aiki da shi. Na gode.
Advertisement

labarai