Connect with us

WASANNI

Najeriya Ta Gayyaci ’Yan Wasa 23 Don Buga Wasa Da Seychelles

Published

on

Kocin tawagar kwallon Najeriya, Super Eagles, Gernot Rohr, ya gayyaci ‘yan wasa 24 don wasan neman shiga gasar kofin Afirka da Najeriya za ta yi da Seychelles a sati mai zuwa.

Cikin jerin ‘yan wasan da aka wallafa a shafin sadarwa na Twitter na hukumar kwallon kafar Najeriya, akwai Odion Ighalo da Ahmed Musa da Henry Onyekuru da Aled Iwobi da Kelechi Ihenacho.

Har ila yau ‘yan wasan gaban da aka gayyata sun hada da Simeone Nwankwo da Samuel Kalu sai kuma ‘yan wasan tsakiya da suka hada da Ogenyi Onazi da John Ogu da Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo da Joel Obi da kuma Kelechi Nwankali.

Cikin wadanda aka gayyato din kuma har da William Ekong da Leon Balogun da Kenneth Omeruo da Bryan Idowu da Chidozie Awaziem da kuma Ola Aina.

Hakazalika a cikin ‘yan wasan bayan da aka gayyato din akwai haifaffen jihar Kaduna, Jamilu Colins, da kuma Semi Ajayi.

Masu tsaron gidan da aka gayyato sun hada da Ikechukwu Ezenwa da Daniel Akpeyi da kuma Francis Uzoho.

Mai koyar da ‘yan wasan kuma ya bayyana cewa ya kirawo matasan ‘yan wasa da yawa domin suma su shigo su bada gudunmawa yadda yakamata sakamakon akwai tsofaffi acikin tawagar da nan gaba kadan zasu daina buga wasa,

“Mu na da matasan ‘yan wasa wadanda nake saran nan gaba zasu zama manyan ‘yan kwallo hakan yasa tun yanzu zamu fara basu dama kafin tsofaffin da muke dasu su tafi” in ji Gernot Rohr.

Ya ci gaba da cewa “Wannan wasan da zamu buga da Seychelles dole ne sai mun samu nasara idan har muna son buga wasan gasar cin kofin nahiyar Africa saboda haka muna bukatar hadin kan kowa”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: