Connect with us

LABARAI

Nakasassasu Sun Yi Zanga zanga A Kan Ayyukan EddonMobil A Jihar Akwa Ibom

Published

on

Kimanin nakasassu hamsin ne suka gudanar da zanga-zanga a kamfanin EddonMobil dake yankin Eket da kuma a kamfanin conglomerate dake yankin  Ibeno cikin jihar Akwa Ibom, inda hakan ya janyo ayyuka suna tsaya chak. Rikicin ya taso nz a ranar talatar data wuce da luaslin karfe hudu na rana a lokacin da suka kullle kofar shiga kalfanin na EddonMobil da kuma inda ake sashen dake  Kua Iboe, inda suka gabatar da bukatar su akan samar masu fa walwala.

An ruwaito cewar, la’aikatan kamfanin sun kasa fita daga harabar kamfanin bayan da suka tashi daga ayyukansu a ranar laraba kuma sukaki barin kofar don ma’aikatan su tafi gidajensu. Sun kuma janyo ayyukan kamfanin suka tsaya chak a ranar alhamis,inda hakan ya sanya mahukuntan kamfanin suka umarci ma’aikatan kada su fita daga kamfanin saboda dalilai na tsaro. Da yake jawkbi a madadin nakasassun Mista Udoh Ekanem ya ce, sunada hakki akan kamfanin na samar masu da ababen more rayuwa da kuma basu horo a karkashin shirin sa.

Ya ce, mu ba lahaukata bane da zamu rufe kamfanin ba lun kuma jima muna son kamfanin ya taimaka mana kamar wadda ya yiwa sauran yan uwanlu dake Bonny,  Fatakwal da kuma Legas.Port Harcourt, and Lagos, amma kamfanin sai akawura yaje ta yi mana da ya kasa cikawa. An kuma ga an jibge jami’an tsaro na yansanda dana farin kaya a kamfanin da rukunonin gidaje na kamfanin dake a Eket da Ibeno.

Kakakin yada labarai na kamfanin Mista  Ogechukwu Udeaga, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar talata ta 25 ga watan Okutoba da kuma ranar 26 na  larabar 2018 a  JB Kua Iboe  dake Ibeno dake  Akwa Ibom, cewar gungun wasu mutane da sunan wakilan  kungiyar ‘Neja Delta Great-Minds’ ta nasassun sun gabatar da zanga-zangar kuma basu sanar da kamfanin akan zanga-zangar ba, kuma hakan ya sanya kamfanin ya damu matuka akan dakatar masa da gudanar da ayyukansa.

A karshe ya ce, tuni mahukuntan kamfanin suka sanar da hukumomin da suka dace akan lamarin.

 
Advertisement

labarai