Daga Rabiu Ali Indabawa
A Somalia farar hula shida sun halaka sakamkon tashin wata nakiya a yau lahadi, kwanakin bayan wani mummunan hari da ya halaka ɗaruruwan mutane. Lamarin ya auku ne lokacin da motar da suke ciki ta taka nakiyar, kamar yadda jami’ai suka faɗa.
Jami’ai a yankin ƙasar da ake kira Lower Shabelle da turanci, sun tabbatarwa Sashen manema labarai a Somaliya cewa, mata biyu da maza huɗu sun mutu bayan fashewar nakiyar, irin wadda aka haɗa a gida ta afkawa wata motar kiya-kiya a ƙauyen da ake kira Daniga, mai tazarar kilomita 35 daga Arewacin birnin Mogadishu.
Muƙaddashin Gwamnan yankin Ali Nur Mohammad ya ce waɗanda harin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne waɗanda suke kai amfani gona kasuwa, kuma suna balaguro ne daga garin da ake kira Afgoye zuwa Bal’ad.
Limamai da jami’an Diflomasiyya sun bayyana baƙin cikinsu kan aukuwar lamarin a lokacin sallar Jumma’a.