Namijin Kokarin Nijeriya A AFCON

Nijeriya

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya sun hada maki hudu a gasar cin kofin nahiyar Afir-ka a bana bayan da suka samu doke Guinea Bissau da ci 2-0 a wasan da kasashen biyu suka buga a daren ranar Laraba.

Kasashen Guinea Bissau da Nijeriya sun buga wasa na uku a cikin rukuni na hudu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Kamaru ranar Laraba kuma wasan da kociyan tawagar Super Eagles ya yi amfani da wadanda ba su samu damar buga wasa ba a wasannin baya guda biyu da kasar ta buga da Masar da Sudan.

Karawar Guinea Bissau da Nijeriya Wannan shi ne karon farko da aka raba raini tsakanin Guinea Bissau da Nijeriya a gasar cin kofin Afirka kuma Guinea Bissau ta yi wasa tara kenan a Afcon ba tare da yin nasara ba, wadda ta yi canjaras uku da shan kashi a shida.

Wadanda ke gaban Guinea Bissau a yawan buga gasar kofin Afirka ba tare da cin wasa ba sun hada da Benin mai 14 da Mozambikue mai 12 da kuma Namibia mai tara sannan Nijeriya ta yi nasara a karawa 12 daga 14 a Afcon da rashin nasara a fafatawa biyu.

Karon farko da Super Eagles ta lashe dukkan karawa uku a cikin rukuni a kofin Afirka shi ne a 2006, sannan Guinea Bissau ba ta zura kwallo ba kawo yanzu a wasannin da ake yi a Kamaru duk da buga kwallo zuwa raga sau 16 da ta yi.

Taiwo Awoniyi ya buga kwallo sau tara na kofar raga, kuma shi ne kan gaba a yawan taba kwallo a da’irar abokiyar karawa sau 14 a wasa biyu a rukuni na hudun.

Exit mobile version