Connect with us

SHARHI

Namun Daji Aminan Bil Adama Ne

Published

on

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kira ga kasar Sin, da sauran kasashe, da su rufe kasuwannin sayar da namun daji masu rai, domin rage kalubalen da bil Adama ke fuskanta.

Kan batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai a birnin Beijing cewa, babu wata kasuwa ta sayar da namun daji masu rai a kasar Sin.

Kana ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta riga ta kafa doka, inda a cikin ta aka tanadi hana farauta, da ciniki, da jigila, da kuma cin namun daji, ya ce kasuwannin sayar da nama, da kayayyakin lambu, da ’ya’yan itatuwa na kasar Sin, ba kasuwannin sayar da namun daji ba ne, kuma duk wanda aka kama yana sayar da namun daji a kasuwanni, za a hukunta shi bisa doka.

Hakika an fara aiwatar da dokar kare namun daji ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin ne daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 1989, makasudin kafa dokar shi ne domin karewa da kuma ceto namun dajin dake neman karewa a doron kasa, haka kuma domin kiyaye daidaiton halittu ta hanyar kare albarkatun namun daji.

Yanzu haka ana fama da masifar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya, bisa sakamakon nazari da binciken da aka samu, an lura cewa, dabbobi ne suka yada kwayar cutar COVID-19 zuwa ga bil Adama, kila bil Adama sun kamu da cutar ne sakamakon cin naman dabbobin daji, amma bai kamata Pompeo ya rika amfani da kalmomi na yaudara ba, yana sukar kasar Sin kamar yadda yake so, har ya baza jita-jitar cewa, ana sayar da namun daji masu rai a kasuwannin kasar Sin.

Namun daji aminan bil Adama ne, bai kamata bil Adama su kashe su ko ci namansu ba, ya dace bil Adama su mutunta namun daji, su yi zaman jituwa tare da su, su kara karfafa gina wayewar kai a fannin kiyaye muhallin halittu, saboda bil Adama da namun daji suna rayuwa kan duniya guda, suna karkashin sararin samaniya mai launin shudi guda, a don haka ana iya cewa, kare namun daji, tamkar kare bil Adama ne su kansu, dole ne a daina aikata laifuffukan farauta, da ciniki, da jigila, da kuma cin namun daji, ta yadda za a tabbatar da muradun bil Adama na kiyaye tsaron halittu, da hana barkewar rikicin kiwon lafiyar jama’a mai tsanani, tare kuma da ba da tabbaci ga tsaron lafiyar rayukan jama’a. (Marubuciya: Jamila Zhou Ta CRI Hausa)

Advertisement

labarai