Nan Da Kwanaki 200 Za A Kaddamar Da Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Sanyi Ta Beijing

Daga CRI Hausa

Nan da kwanaki 200 za a kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing.

A ranar 7 ga watan Mayun bana, yayin hira da shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic ta kasa da kasa (IOC) Thomas Bach, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana da imanin cewa, za ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi cikin nasara, kuma tana fatan yin hadin gwiwa da kwamitin IOC domin tabbatar da gudanarwar da gasar kamar yadda ake fata a birnin Beijing.

Kasar Sin za ta gudanar da gasar bisa ka’idojin kare muhalli, da kiyaye tsaro, da bude kofa ga waje, da kuma tsimin kudade, kuma, za ta maida hankali kan aikin kandagarkin annobar cutar COVID-19.

Gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi shi ne fatan al’ummomin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya kuma maida hankali matuka kan ayyukan gudanar da gasar, inda ya yi kira da tsara gasar ba tare da barnata kudade ba.

Haka kuma, ya bukaci a tabbatar da tsaron gudanar da gasar yadda ya kamata, da kuma kyautata matakan rigakafin yaduwar annoba, da gobara, da sauran haddura, domin tabbatar da gudanar da gasar wasanni cikin kwanciyar hankali. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version