Nan Da Shekara 12 Za A Daina Samun Wadanda Ke Dauke Da Cutar Kanjamau –Dakta Usman

Nan da shekara uku zuwa biyar ana sa ran samo rigakafin wannan cutar Kanjamau

Dakta Usman Bashir shi ne shugaban hukumar dakile yaduwar  Kanjamau a Jihar Kano, malami a sashin koyar da dalibai likitoci cutukan jiki na Jami’ar Bayero dake Jihar Kano, shugaban Hukumar dakile cutar Kanjamau a Jihar Kano. Atattaunawarsa da wakilanmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA da NA’IMA ABUBAKAR, Alhaji Bashir Usman ya bayyana shirin da hukumarsa ta ken a ganin an dakile yaduwar wannan cuta mai karya garkuwar jiki, sannan kuma ya ja hankalin jama’a wajen halartar asibitoci domin duba lafiyarsu data iyalansu. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance. Za muso jin suna da takaitaccen tarihin Rayuwa?

Alhamdulilahi ni sunana Usman Bashir haifaffen Jihar Kano nayi karatuttuka na tun daga matakin ilimin firamare har zuwa Jami’a cikin kasar nan ban fita zuwa wasu kasashe ba,haka kafin kama wannan aiki malami ne a Jami’ar Bayero d ake Kano, wanda nake koyar da dalibai ilimi sassan jikin bil’adama, a halin yanzu kuma nine shugaban hukumar dakile ya duwar cutar Kanjamau a Jihar Kano.  Wannan shi ne tarihi na a ta kaitaccen tarihin Rayuwa ta.

 

Mene ne muhimman ayyukan da aka rataya a wuyan wannan hukuma?

Kamar yadda aka sani wannan hukuma an kirkireta a shekaru bakwai da suka wuce, kasancewar a baya wasu kungiyoyi ne ke daukar nauyin yawi da wannan cuta , kuma akwai tsarin da ake bi wanda ke tabbatar da cewa akwai lokacin da zaizo dole hukumomn kasa su maye gurbi wadncan kungiyoyi. Alhamdulillahi yanzu an fara tafiya a hankali wanda abaya ba muda wani kasafin kudin gudanar da wannan hukuma, amma yanzu an shigar da wannan hukuma cikin kasafin kudi wanda duk shekara za a ci gaba da ware wani kaso da ci gaba da gudanar da ayyukan wannan hukuma. Musamman ganin kungiyoyin da suke taimkaawa abaya sun tafi yanzu dole Gwamnati ce zata ja ragamar ci gaba da gudanar da wannan aiki.

Kamar yadda aka sani ita wannan cuta ba wai bada magani kadai ta sa a gaba ba, har da gano sabbin wadanda suka kamu  da wannan cuta domin ganin an rage yaduwarta, yanzu muna asibitoci guda 53 da muke  bada magani kyauta a cikinsu, sannan kuma muna da wasu asibitocin guda 494 da ake gudanar da gwaje gwajen wannan cuta a fadin Jihar Kano, kuma wadannan sun hada da asibitocin gwamnati d akuma masu zaman kansu. Sai kuma kananan asibitoci da gwaji ake kawai na masu ciki ko wani ya zo d awasu alamun kamuwa da cutar ko yazo kawai domin a gwada shi da sauransu , idan an gwada aka samu yana da wannan cuta sai tura shi asibiti domin dorashi akan magani. Haka kuma yanzu akwai sabon tsarin da aka bujiro dashi wanda ake kira da gwaji da kuma bada magani (Test and treat). Wanda abaya kafin zuwan wannan tsari sai anyi gwaje gwaje an gano karfin cutar idan cutar bata kai wani matsayi ba ba dole sai an bashi magani ba. Yanzu bincike ya nuna masu shan maganin wannan cuta basa yada ta sosai, saboda sai aka ce to ya za a bar mutane suna dauke da ita kuma suna yawo a gari, yafi da cewa a dora su akan magani yadda kafin asamo maganin wannan cuta karfin cutar ya ragu a jikinsu.

 

Kenan har yanzu ba’a samu maganin wannan cuta mai karya garkuwar jiki ba?

Kaamar yadda muka sani akwai wasu kwayoyin cuta da ake kira Birus, Bacteria da sauransu daman ire iren wadannan kwayoyi tun asali idan sun kama mutum basu da magani, sune irinsu kyanda, Polio da bakon dauro, saboda haka wanda bay a dauke da irin wadannan cutka su ake yiwa rigakafi kuma yawanci rigafi sau daya ake yenta wanda insha Allah idan dai an samu an yiwa mutum matukar anyi masa alokacin day a kamata ba zai kamu da waccan cuta ba. Haka itama wannan cuta Kanjamau ana nan ana ci gaba da bincike  wanda ake fatan nan da shekara 12 za a dai na samun wadanda ke dauke da wannan cuta, domin wanda duk ke dauke da wannan cutar an dakile yaduwarta .

Haka kuma nan da shekara uku zuwa biyar ana sa ran samo rigakafin wannan cutar Kanjamau, ana nan ana gudanar da bincike a kasar afirika ta Kudu, kuma binciken na nuna alamu masu kyau na samun rigakafin wannan cuta  saboda haka da zarar an tabbatar da ingancin wannan allura za fara yin rigakafinta kenan ka ga mutane sun samu kandagarkin cutar. Ya yinda shi kuma wanda ke dauke da ita baya yada ta.

Likita idan akayi la’akari da

jihar Kano mai dauke yawan al’umma, shin  wane mataki Jihar Kano ke kai na wadanda ke dauke da wannan cuta?

Kamar yadda aka sani Jihar na da yawan al’ummar da suka kai mutum Miliyon 16-17 kuma bisa kiyasin alkalumanmu ya nuna cewa   kasha 2% cikin dari ke dauke da wannan cuta a Jihar Kano kwatankwacin mutum 280,000 kenan, ka ga adadin yana da yawa. Za tara da wasu jihohin na kiyasin 7% zuwa 8%, amma idan ka duba yawan jama’arsu sai ka tarar bas u wuce  mutum  miliyon biyu ne, saboda haka idan ka cire wancan kiyasi daga cikin wannan adadi sai katarar  har yanzu akwai tazara mai yawa tsakaninmu dasu. Kuma Jihar Kano wuri ne kasuwanci da kuma hada-hada itama kuma wannan cuta tafi yaduwa wurin da ake gudanar da irin wannan hada hada ake wasu harkoki wanda idan ba kawo wasu tsare tsare ba dole a samu matsala.

Alhamdulillahi mu anan JIhar Ksno mun samar da tsaruka masu yawa muna kai maganunuwa  da sauran kayan aiki irin na gwaje gwaje. Wani ci gaba kuma kwanan nan muke fatan kaiwa majalisar dokokin Jihar Kano wani kudiri  wanda zai tabbatar da cewa wanda duk zai yi aure ya kamata ayi masa gwaji ba kuma na Kanjamau kadai ba harda cutuka irin cutar sankarar jini kamar yadda sauran makwabtanmu irinsu Jigawa, Katsina da Kaduna duk sun samar da irin wannan dokoki wanda duk lokacin da za ay aure sai kawo takardar shaidar gwajin jini.

 

Kasancewar  Jihar Kano mai kananan hukumomi  44 shin ko wace hanya wannan hukuma ke bi wajen isar da irin wannan sako ga al ‘ummar mu na karkara?

Alhamdulillahi kamar yadda kasan  jama’ar Kano akwai sauraren kafafen yada labarai wannan tasa muke amfani kafofin sadarwa wajen isar da duk wani sako da muke fatan aikawa jama’a, hwar aka kuma kasancewar yanzu haka tare muke da ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano mu ba asibitoci ne da mu ba, muna bayar da ilimin harkokin lafiya ne kamar sanin makamar aiki ga ma’aikatan lafiya tare da kai kayan aiki tare hadin guiwar kungiyoyin sa kai da suke taimakamana. Musammman wajen batun gwaje gwaje da bayanai musamman wadanda ke dauke da irin wannan cuta za su yiwa Jama’a bayanin cewa suna dauke da wannan cuta kuma ga irin tallafin da ake mana jama’a kuma zasu ga yadda suke cikin kuzari.

Haka kuma muna da ma’aikata wadanda muka wadata da kayan aiki irinsu kwamfuta wadanda ke sanar da mu duk halin da ake ciki na ci gaba ko akasin haka, mun  baiwa sama da mutun 500 horo akan wannan aiki,

 

Ya ya dangantaka ta ke tsakanin wannan hukuma da kungiyar wadanda ke  dauke da wanann cuta?

Alhamdulillahi zuwa na wannan wuri na zauna da masu dauke da wannan cuta inda na shaida masu cewar mu aikinsu muka zo yi,  ko kwanan nan da aka gudanar da ranar masu dauke da wannan cuta tare muka gudanar da shirye shirye dasu a kafafen yada labarai haka kuma bara makananan hukumomi 14 muka shrya gangami tare dasu tare da gudanar da gwaje gwaje sukan taimaka mana wajen yiwa jama’a bayani. A duk inda muka zauna dasu suka kan fadi irin taimakon da ake masu da kuma bayyana mana irin matsalolin da suke fuskanta wanda kuma muke yin duk mai yiwuwa wajen magance su.

 

Ta bangaren Gwamnatin ya dangatake gudana tsakanin wannan hukuma da Gwamnati?

Alhamdulilahi ba abinda zamu ce da Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje sai godiya domin tana baiwa wannan hukuma gudunmawa  ga harkokin lafiya kwarai da gaske, bara kadai gwamnati ta sahalle mana kashe kiyasin kudi sama da Naira Miliyon 400 da doriya, wanda muka sayo kayan gwaje gwaje musamman wasu manyan mashina wanda muka guda a Doguwa, Gwarzo da Wudil wanda abaya sai an shigo cikin gari ake samun wadannan kayan aiki.

Haka kuma mun sayi kwmafutoci mun rabawa ma’aikatanmu masu gudanar mana da kididdiga sai gudanar bitoci ga mutane sama da 500 sanin makamar aiki, duba kaga ana ofis da hasken wutar lantarki muke amfani domin kaucewa katsewar hasken wutar lantarki ga kuma motocin aiki wadatattu, duk wannan Gwamnatin Kano ta samar mana dasu.

 

Ya mutum zai iya fahimtar yadda ake kamuwa da cutar Kanjamau?

Bayan amfani da kafafen yada labarai muna samar da takardu wanda ake kafewa a wuraren haduwar jama’a wanda ake rubutawa da turanci, hausa da kuma ajami. Kamar yadda muke cewa Saduwa ta hanyar jima’I, yank an farce, aski, kaho, cire beli, tsagun gargajiya, sa jini ko daukarsa da kuma wajen haihuwa kamar yadda muka ambata a baya. Muna shaidawa jama’a wadannan hanyoyin kamuwa da cutar sannan kuma muna fadakar dasu hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar.

 

 

Exit mobile version