Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta yi kiga ga gwamnatin tarayya da kungiyoyin malamai da su zauna tuburin sulhu domin shawo kan matsalar yajin aikin da malaman jami’o’i ke ci gaba da yi a halin yanzu. Mataimakin shugaban kungiyar dalibai ta kasa Kwamared Shattima Umar ne yayi wannan kiran a wani taron manema labaru da ya Kira kan bahasin babban taron da suka yi a Bauchi kan tattalin arziki, tsaro da kuma ci gaban kasa a kwanakin baya.
Ya ci gaba da cewa “NANS tana kira ga gwamnatin tarayya da malamai da su zauna waje goda domin ganin an kawo karshen wannan yajin aikin da ake ta fama da shi. Domin dalibai suna gida alhali daf wasu zasu fara jarabawa kuma sai ga shi malamai sun zunduma yajin aiki. Muna kira ga gwamnati da malamanmu da su taimaka mana mu dalibai su dawo su sasanta domin ilimi ya ci gaba da tafiya yanda ya kamata a kasar nan”. In ji shugaban NANS
Shatti Umar ya kuma jinjina wa kokarin da gwamnatin tarayya take yi wajen inganta tsaro a makarantu sai ya bukaci gwamnati da ta kara himma domin daliban su kasance masu samun amince a lokacin da suke ajujuwan daukan darasin nasu.
Haka kuma ya yi Kira ga gwamnati, da ‘yansiyasa da sauran bangarorin da abin ya shafa da cewar su bar matasa suna shiga komai domin a dama da su a cewarsa hakan ne zai sanya kasa ta ci gaba “Ya kamata gwamnati ta bar matasa suma su shiga ana damawa da su wajen fadin ra’ayinsu, kuma ya zama da matasa ne ake gudanar da gwamnati haka su ma bangarorin ‘yan siyasa ina kira da su shigar da matasa wajen tafiyar da kasar nan. Yana da kyau ‘yan siyasa su rage kudin fom domin matasa su samu su saya don a dama da su a fagen siyasa”.
Ya kara da cewa “Muna jinjina wa majalisar tarayyar Nijeriya a bisa kawo kudirin da zai bai wa matasa damar shiga takarar siyasa. Muna kira ga shugaban Nijeriya da ya sa hanu kan wannan kudirin domin matasa su ma a dama da su wajen shugabacin kasar nan”. In ji Shattima
Kwamared Umar Shattiman ya kuma jinjina wa gudummowar da gwamnatin jihar Bauchi ta ba su wajen tallafa musu kan babban taron da suka gudanar a Bauchin “muna godiya wa gwamnan jihar Bauchi kan tsayawa da yake yi kan tallafa wa dalibai a kowane bangare, muna kuma kira ga sauran gwamnoni da su yi koyi da irin halin gwamnan jihar ta Bauchi kan tallafa wa dalibai”.
Mukadashin Shugaban kungiyar dalibai ta kasa ya ce kimanin daliban sama da miliyan 41 ne suke karkashin shugabancinsu, don haka, da bukatar gwamnati ta yi la’akari da yawansu domin shigar da su cikin al’amurar rayuwa, domin wasu daga cikinsu Allah ya yi musu baiwar tafiyar da al’amurar mulki, da siyasa da sauransu