Kungiyar kwallon kafa ta Napoli dake buga gasar Siriya A ta kasar Italiya ta tabbatar da cewa za a sake yi wa dan wasanta na gaba, victor Osimhen gwajin cutar coronabirus, saboda har yanzu cutar ba ta rabu da shi ba.
Gwanji ya tabbatar dan wasan mai shekarau 22 ya harbu da cutar cobid 19 ne jim kadan bayan dawowarsa daga kasarsa, Najeriya, inda ya je hutun Kiristimeti kuma tuni aka killace shi kamar yadda dokar hukumar lafiyar kasar ta tanada.
An yi zargin cewa dan wasan ya kamu da wannan cuta ne sakamakon yin watsi da ka’idojin da aka gindaya domin dakile ta, a yayin da ya yi bikin tunawa da ranar haihuwarsa a ranar 29 ga watan Disamba, lamarin da ya nemi afuwa a kai.
dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriyar ya kebe kansa na tsawon kwanaki 14, amma bayan an sake gwada shi sai aka ga burbushin cutar a tattare da shi wanda yake nuna cewa cutar tana tare dashi har yanzu.
kungiyar Napoli ta rubuta a shafinta na Twitter cewa za a sake yi wa dan wasan gwajin Cobid 19 kamar yadda likitoci suka bayar da shawara kuma shima dan wasan tun farko ya bukaci hakan domin yadda ya damu ya koma domin ci gaba da buga wasa.