Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta nada tsohon kociyan AC Milan, Gennaro Gattuso, a matsayin sabon kociyanta bayan korar Carlo Ancelotti da ta yi a ranar Talata sa’o’i bayan nasarar da ya samu kan kungiyar Genk da ci 4-0 wanda ya bai wa Napolin damar tsallakawa zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League.
Gattuso mai shekara 41, shi ne tsohon kociyan AC Milan kuma ya bar kungiyar ne a karshen kakar wasanni ta bara sakamakon rashin tabuka abin azo a gani wanda yasan kungiyar ta kare a mataki na tara.
Napoli dai na matsayi na bakwai ne a yanzu a gasar Siriya A da maki takwas tsakaninta da kungiyar da ke matsayi na hudu a jadawali wanda hakan yake nufin idan aka cigaba da tafiya a haka ba zata samu damar zuwa kofin zakarun turai ba
“Akwai bukatar mu zage dantse mu yi aiki da kyau domin ganin mun samu nasara a wannan lokacin saboda ba kawai mai koyarwa bane yake aiki domin a samu nasara suma ‘yan wasa da shugabanni tare da magoya baya duka sai sunyi aiki da gaske” In ji Gattuso.
Manufar dauko sabon kociyan dai a yanzu ita ce, dawo da makin da kungiyar ta yi asara a baya domin komawa gasar Zakarun Turai a shekara mai zuwa wanda kuma shugaban kungiyar, yake ganin Gattuso zai iya wannan aiki.
Gattuso ya buga kwallo karkashin koyarwar Ancelloti a AC Milan ya kuma ce, kamar mahaifi yake a wajensa kuma da shakuwa sosai kuma yana taimaka masa sannan a cewar Gattuso Ancelotti ya samu dukkan nasara kuma shima yana bukatar aiki sosai domin samun irinta a rayuwa.