Muhammad Maitela" />

NAPPS Ta Zabi Sabbin Shugabani A Jihar Yobe

A ranar Asabar, hadaddiyar kungiyar masu gudanar da makamantu masu zaman kan su ta kasa, reshen karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe, ta zabi sabbin shugabanin ta, wadanda za su ja ragamar kungiyar, shekaru hudu masu zuwa.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben, jami’in da ya jagoranci gudanar da zaben NAPPS 2019, Usman Alhaj Saleh ya bayyana cewa kungiyar tana da mutane 88 da suka cancanci jefa kuri’a, a gundumar Potiskum, yayin da kuma mutum 55 ne suka jefa kuri’a a lokacin zaben, tare da guda biyar (5) wadanda aka kada ba bisa ka’ida ba (invalid).

Bugu da kari kuma, jami’in zaben ya bayyana Alhaji Ahmadu Bukar a matsayin wanda ya lashe zaben  kuri’a 37, sai kuma Fatima B. Umar wadda aka zaba a matsayin mataimakiyar shugaba da Mohammed Sherrif a matsayin jami’in jin dadin jama’a a kungiyar.

Sauran sun hada da Mustapha Ibrahim jami’in kula da jin dadin jama’a na biyu, sai Malam Ali Idi wanda ya dare kujerar babban sakataren kungiyar da Adamu Saleh mataimakin sakatare da Aliyu Idriss Tikau wanda zai rike jami’in hulda da jama’a sai Musa B. Ibrahim a matsayin ma’aji tare da Mohammed Sambo da zai rike ofishin sakataren kudi, sai mukamin mai binciken kudi da ya fada hannun Ibrahim Ali Bomoi.

Haka zalika kuma, kungiyar ta gudanar da wannan zaben a dakin taron ofishin sakataren ilimin karamar hukumar Potiskum tare da isasshen tsaro da masu sa ido daga bangarori daban-daban.

Da ya ke jawabin godiya, jim kadan da bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben, Ahmadu Bukar ya bayyana cewa sabbin zubin majalisar zartaswar kungiyar zai tabbatar wajen ganin ya hada kan ya’yan kungiyar don cigabanta.

“Wanda za mu tabbatar wajen ganin kowace makaranta mai zaman kanta ta samu wakilci a duk wani al’amarin da ya taso, kuma za mu rike gaskiya da adalci wajen bunkasa ayyukan koyarwa tare da yin aiki tukuru wajen ganin ma’aikatan mu suna gudanar da aikin su bisa ka’ida.

“Bugu da kari kuma, za mu yi kokarin fadakar da jama’a tare da gwamnati wajen canja ra’ayin kallon da su ke yi wa makarantu masu zaman kan su, za mu aiwatar da hakan ta hanyar dinke wasu baraka tare da yukurin da kungiyar NAPPS ke yi wanda zai bayar da zarafin da za su goya mana baya a bangarorin da muke da bukatar hakan,” in ji shi.

A hannu guda kuma ya ce, NAPPS ya bukaci gwamnati ta samar da yanayin da bunkasa ma’aikata da habaka makarantu masu zaman kansu a kasar  nan, domin yin gogayya da takwarorin su na wasu kasashen duniya.

Ya ce, “Yanzu haka muna kokarin hada hannu da ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar Yobe don bunkasa wadannan makarantu.”

Exit mobile version