NAPTIP Ta Bankado Masana’antar Sayar Da Jarirai A Abuja

Hukumar yaki da Fataucin Mutane (NAPTIP) ta sanar da killace wani haramtacce asibiti da ake safarar jarirai a unguwan Nyanya na yankin babban birnin tarayyar kasar nan, bayanin haka ya fito ne a wata takarda da jami’in watsa labaran Hukumar Josiah Emerole, ya sanya wa hannu a Abuja ranar Lahadi,

Mista Emerole ya ce, makwannin da suka wuce ne Hukumar NAPTIP ta kama shugaban asibitin safarar jariran bayan ya cuci wasu mata da suke tsananin bukatar jarirai.

Ya ce, kama asibitin mai suna Akuchi Herbal Concept, dake kusa da gidan ruwa a Sabuwar Nyanya a yankin Abuja na cikin binciken da hukumar ke yi ne na bakalar safarar jarirai  a yankin babban birnin tarayya Abuja, abin da jawo hankalin ‘yan Nijeriya musamman ‘yanuwan wadanda suka bata a lokuttan baya.

I dan za a iya tunawa, a makon da ya wuce ne jami’an NAPTIP suka kama wani boka dan shekara 38 da laifin yaudaran mata masu neman haihuwa, ya kan yi wani siddabaru ne sai matan su ga kamar suna da juna biyu, daga baya sai ya basu jariran daya sato na wasu mutane ya kuma karbi makudan kudi a hannunsu.

Wanda aka kaman dan jihar Enugu ne, shi ne kuma ke da asibitin Akuchi Herbal Concept dake Sabuwar Nyanya a Abuja, an kuma samu nasarar kama shi ne bayan binciken hadin gwiwa tsakanin jami’an Hukumar dana DSS.

Jami’in watsa labaran ya ce, an gudanar da wannan samamen ne a bisa umarnin shugaban Hukumar Julie Okah- Donli , shugaban sashen bincike na Hukumar, “An gano wasu layu da magunguna da ake ba mata don ya sa su rinka jin kamar suna da juna biyu, da kuma ganyayyaki na tsafi da sauran su”

Shugabar hukumar ta ce, ana ci gaba da bincike domin gano tsananin girman laifin da wanda ake zargin ya aikata. “Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin laifuffukan da ake aikatawa a  wurin domin daukan matakin daya dace”.

“Wannan na cikin kudirinmu na gani ba a cuci wani dan Nijeriya ba” in ji ta.

Exit mobile version