An bayyana gagarumar nasarar da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu da cewa nasara ce ta al’ummar Jihar Kano, musamman batun zaman lafiyar da al’ummar Kano ke kwankwada alokadin da wasu Jihohi barci ma ke gagararsu. Jawabin haka ya fito daga bakin shugaban Hukumar bada tallafin Karatu ta Jihar Kano, Abubakar Zakari, kuma wanda a halin yanzu aka sahalewa yiwa Karamar Hukumar Tarauni takarar shugabancin Karamar Hukumar a zaben da za’a gudanar nan gaba kadan.
Habu P.A ya ci gaba da cewa ko hasidin iza hasada ya sallamawa Khadimul Islam, Musamman idan ana batun zaman lafiya, wanda masana da masu bincike suka hakkake cewar Jihar Kano ce jihar data zarta jihohin kasarnan Ingantaccen zaman lafiya. Wannan babu shakka ya samu ne sakamakon kyakkyawan hadin kan da al’ummar Kano ke baiwa kyawawan munufofin Gwamnati.
Da ya ke tsokaci kan batun takarar shugabancin Karamar Hukumar Tarauni da aka amince da cewa shi ne aka aminta da yin takarar, cewa ya yi, wannan kuma wata baiwa ce daga Allah ba wayona bane. Don Haka sai ya jinjinawa shugabbancin Jam’iyyar a matakin Karamar Hukuma da kuma Jiha, sannan ya godewa Wakilin al’ummar Tarauni a Majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Hafiz Kawu da dukkanin masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar ta Tarauni bisa kyautata min zato da a ka yi, in ji Habu PA.
Saboda Haka sai Ababakar Zakari ya bukaci wadanda suka nuna sha’awar yin wannan takara kuma Allah yasa shi ne ya zama maslaha da cewa su taho ayi aiki tare domin samun nasarar Jam’iyyar APC a kakar zaben da ake Shirin gudanarwa a Shekara mai zuwa.