Abdullahi Muhammad Sheka" />

Nasarar Ganduje ‘Yar Manuniya Ce Ga Wanzuwar Dimukradiyyar Nijeriya – Kadawa

A kullum demokaradiyyar kasar nan kara balaga take yi tare mallakar hankalin Kanta, musamman idan aka yi la’akari da yadda al’umma ke kara samun wayewa ta fuskar lalubo wadanda suka hakikance da cewa, za su kula da harkokin cigaban rayuwarsu. Hakan ta sa yanzu jama’a suka sanya tabaran hangen nesa domin zakulo mutanen da suke ganin idan an zabe su, kwalliya na iya biyan kudin Sabulu.

Bayanin haka, ya fito ne daga bakin Matashi kuma jajirtaccen Dan kishin kasa, Alhaji Abubakar Salisu Kadawa, a lokacin da yake zantawa da mane ma labarai jim kadan bayan isowar Gwamna Ganduje, filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, bayan dawowarsa daga ziyarar aiki wanda ya raka  Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,  zuwa Kasar Afirka ta Kudu.

Kadawa ya kara da cewa, ganin yadda al’umma suka yi wa filin jiragen saman na Malam Aminu Kano kawanya, wannan kadai ya isa ya tabbatar da cewa yanzu an  daina daure al’umma da igiyar zato, kuma kamar yadda a ka sani ne jama’ar Jihar Kano, idanunsu a bude ya ke sarai ba wai makafi ba ne, a cewar tasa.

Sannan ya cigaba da cewa, hukuncin da Kotun sauraron korage-korafen zabe ta zartar a shari’ar da Jam’iyyar PDP da Dan takararta, Abba Kabir Yusif ya gabatar inda su ke kalubalantar sahihancin nasarar Gwamna Ganduje da cewa, fargar jaji ce kawai. Mai shari’ar wadda ta nuna kwarewa tare da sadaukar da kai wajen tsage gaskiya ko mai dacinta.

Babu shakka, wannan hukunci ya fito da gaskiyar abubawan da suka jima suna ta da hankalin al’umma, musamman yadda masu adawa da gwamnati ke ta faman yamadidin cewa, wasu manyan Jami’an Gwamnatin Ganduje ne suka ya ga takardun zabe a mazabar yankin Gama.

“Alhamdulillahi, sai ga shi yanzu gaskiya ta yi halinta an bayyana wanda ya ya ga takardun sakamakon zaben na Gama, don haka jama’ar Jihar Kano suke cike da farin ciki da jin wannan hukunci na Kotu, muna kara yi wa Allah godiya, bisa wannan nasara da Gwamna ya samu wadda dama mu ba mu yi mamaki da ita ba, musamman idan aka yi la’akari da ingantattun tsaren-tsaren wannan gwamnati, day a hada da batun ilimi kyauta, samar da Ruga domin makiyaya, samar da katafariyar Cibiyar koyar da sana’o’i ga Matasa da kuma tabbatar da amincewa da biyan mafi karancin albashi ga Ma’aikatan Jihar Kano da dai sauran makamantansu”, in ji shi.

Bugu da kari a cewar tasa, tuni yanzu jama’a sun gamsu da cewa demokaradiyyar Nijeriya ta fara Balaga, don haka masu hangen nesa sun sa tabaran hangen nesa domin hango duk wata kura da ake shirin lullubo ta da fatar akuya, ganin yadda bayan sanar da hukuncin Kotun jama’ar Kano duk da irin farin cikin da suke ciki amma sai aka yi abinda ya dace wajen nuna dattako a lokacin nuna murnar samun wannan nasara.

Har ila yau, da yake yin tsokaci akan kiraye-kirayen da aka fara ji akan wanda zai gaji buzun Khadimul Islam, sannan wasu ke ganin kamar Sanatan Kano ta Arewa ne ya fi da cewa da zama Khalifan, Kadawa cewa ya yi shi ido ba mudu ba ai ya san kima, domin kuwa Hon. Barau I Jibrin ya cika dukkanin ka’idoji da kuma nagartar da ake bukata ga dukkanin wadanda ke fatan gadar wannan buzu na Gwamna Ganduje. “Amma dai muna kara kira ga Jama’a da a cigaba da baiwa wannan gwamnati cikakken goyon baya, kasancewar har yanzu akwai sauran lokaci, musamman ganin yadda shi Gwaman da Sanata Barau, abinda suka mayar da hankali shi ne hada kan al’umma tare da cigaba da kwararo ayyukan alhairi ga Kanawa.

Daga nan, sai Salisu Kadawa ya kara jinjinawa dandazon Matasa musamman na Karamar Hukumar Kumbotso, bisa kokarin da suke yi na ganin an samu kyakkyawan sauyi. Matashi kamar yadda aka tabbatar sai da aka kai ruwa rana kafin a baya ya amince da bukatar al’ummar Kumbotso na fitowa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Karamar Hukumar Kumbotso, an ji yadda sai ta kai ga Matasa sun gama shirin gurfanar da shi gaban Kuliya matukar ya ki amsa wannan kira.

Wani abin sha’awa ga wannan Matashi shi ne, yadda bai taba rike wani mukami a Siyasance ba, amma alhairansa sun mamaye Karamar Hukumar Kumkotso da kewayenta, duk wanda ya kwana kuma ya tsahi a Karamar Hukumar ta Kumbotso ya ga irin gudunmawar da ya ke bayarwa. musamman a lokacin azumin watan Ramadan da kuma taimakawa Marayu da wadanda suka gamu da wata matsala. Wannan tasa al’ummar Kumboso suka ce tsakaninsu da Abubakar Salisu Kadawa mutu-ka-raba.

Wasu masu hangen nesa cikin dattawan Karamar Hukumar Kumbotso, sun bayyana cewa sun jima ba su ga Matashi mai ladabi tare da girmama na gaba da shi kamar Abubakar Kadawa ba, domin ya banbanta da sauran wadanda idan ka gan su a kofar gidanka, sai lokacin da bukatarka ta taso. Idan bukatarsu ta biya shikenan sai su yi dibar karan mahaukaciya da kowa.

Exit mobile version