Connect with us

RAHOTANNI

Nasarar Hakan Ma’adanai Na Tattare da Hadin Kan Al’umma Ne , Inji Gwamnatin Tarayya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar, kamfanonin da basu shafi fannin hakara ma’adanai a kasar nan suna aiwatar da ayyukansu ba tare da kulla yarjejeniya da alumomin da suke zaune a inda ma’adanan suke ba.  Daya daga cikin wakilan kwamitin kula da muhalli Mista Osseini Ukwenya ne ya sanar da hakan a a taron bita a tsakanin masu hakar ma’adanai da alumomin dake yankin Bwari a babban birnin tarayyar Abuja. A cikin sanarwar da ma’aikatar hakar ma’adanai da karafa ta kasa ta fitar a ranar Litinin data wuce a Abuja  an ruwaito Ukwenya yana cewa yarjejeniyar da alumomin tanada mahimmancin gaske wajen gudanar da aikin hakar ma’adanai kamar yadda dokar ta hakar ma’adanai ta tanadar. Ukwenya yaci gaba da cewar, ta hanyar kulla yarjejeniyar, masu hakar zasufi bawa alumomin hakkin su kuma hakkin kwamitin newajen ganin anbi ka’ida da masu hakar suka sanya wa hannu, inda ya yi nuni da cewar, yarjejeniya tsakanin masu hakar ma’adanan da alumomin bata wuce ba domin wani abunbe da za’a iya yenta a cikin ruwan sanyi tare da masu ruwa da tsaki. Ukwenya, wanda kuma shi ne jaimi’in karbar koke na akan hakara ma’adanai na Abuja ya ce, hakar ma’adanan da akayi ta ba bisa ka’ida ba, dole ne a biya alumma diyya. Ya bayyana cewar, koken da alumma suke yi shi ne na yadda ake gurbata masu yanayi. Kwamitin ya kuma ya bayar da shawara a kan yadda za’a kiye a kan gurbata muhalli da aydda za’a rage hakan zuwa wani matsayi. Ukwenya yaci gaba da cewar, akwai maganganun daya kamataa a shawo kansu dake a cikin dokar ta hakar ma’adanai wanda wannan shine kwamtin yake son shawo kai a bisa korafe-korafen da kwamitn ya karba daga alumomi akan masu hakar ma’adanan.Yace, “zamu yi kokarin hada karafe-korafen don yanke hukuncin daya dace kuma hakan ne ya sanya muka kirawo wannan taron yadda alumomin suma zasu amfana. Ukwenya ya yi kira gaalumomin da suka fusata dasu bi hanyoyin dasuka dace ta hanyar kai kokensu ga mahukunta, musamman ga kawamitin don a tabbatar babu wanda ya dauki dpka a hannunsa

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: