Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Nasarar Harba Tauraron Dan Adam Na Beidou Na Karshe Ta Shaida Ci Gaban Sin Wajen Kirkire-Kirkiren Kimiyya Da Fasaha

Published

on

A safiyar yau Talata 23 ga wata, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na BeiDou na karshe, lamarin da ya alamta cewa, an kammala aikin jibge taurarin dan Adam masu shawagi na Beidou a fadin duniya daga duk fannoni, wannan yana da ma’ana ta musamman a tarihin ci gaban aikin zirga-zirgar sararin samaniya da kimiyya da fasaha, haka kuma zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya ta hanyar samar da goyon baya ga fannin kimiyya da fasaha.

Tun daga shekarar 1994, lokacin da aka fara kera tauraron bil Adam na farko na BeiDou, har zuwa yanzu da aka yi nasarar harba tauraron bil Adam na BeiDou na karshe, kasar Sin ta shafe tsawon shekaru 26, abun farin ciki shi ne ta samu ci gaba mai faranta rai a mataki daban daban, wato daga mataki na samar da hidima ga kasar Sin, zuwa mataki na samar da hidima ga kasashen Asiya da tekun Pasifik, har zuwa mataki na uku wato samar da hidima ga daukacin kasashen duniya, yanzu haka tsarin shawagi na BeiDou na kasar Sin, yana daya daga cikin manyan tsare-tsaren shawagi na duniya guda hudu, wato sauran uku sun hada GPS na Amurka da Glonass na Rasha da kuma Galileo na Turai.
A matsayinsa na babban ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha, tsarin BeiDou ya hada sadarwa da shawagi waje daya, ana iya cewa, nasarar da kasar Sin ta samu ta shaidawa al’ummun kasa da kasa cewa, kasar Sin tana gudanar da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha bisa dogaro da kanta ba tare da rufa rufa ba.
Tsarin shawagin BeiDou shi ne muhimmin sashin more rayuwar jama’a na farko da kasar Sin ta samarwa al’ummun kasa da kasa, ko shakka babu tsarin zai taimaka wa ci gaban kasashen duniya, musamman ma a bangarorin ba da ceto ga wadanda suka shiga wahala sakamakon masifu, da kandagarkin yaduwar annoba, da kuma sauye-sauyen tsarin tattalin arziki.
Da farko, tsarin BeiDou yana da fannoni uku wato ba da shawagi da samar da lokaci da kuma sadarwa, zai kuma samar da hidima mai inganci ga sufuri, da aikin gona, da aikin gandun daji, da samar da bayanan yanayi, da sadarwa da sauran su, tabbas tsarin, zai taka rawa wajen ci gaban zaman takewar al’ummar kasashen duniya.
Kana tsarin BeiDou yana samar da hidimar sadarwa cikin sauri tsakanin masu amfani da tsarin a wurare daban daban, misali yayin da kasar Sin ke kokarin dakile annobar cutar COVID-19 a bana, tsarin BeiDou ya taka rawar gani a bangaren samar da bayanai a kan lokaci.
Abu mafi muhimmanci shi ne a daidai wannan lokacin da muke ciki, tsarin BeiDou da fasahar 5G da AI da sauran fasahohin zamani suna sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a shekarar 2019, adadin kudin da aka kashe kan ayyukan dake da nasaba da tsarin BeiDou ya kai kudin Sin yuan biliyan 350, kana an kimmanta cewa, zai karu da kaso 20 cikin dari a cikin watanni masu zuwa.
A halin yanzu rabin kasashen duniya suna amfani da tsarin BeiDou, muna sa ran cewa, sana’o’in dake shafar tsarin za su ingiza sabon ci gaban tattalin arzikin duniya.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai