Connect with us

WASANNI

Nasararmu Ta Dawo – Arteta

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa nasarar kungiyar ta dawo bayan da tawagar tasa ta samu nasarar lashe wasanni biyu a jere tun bayan da aka koma buga wasanni a kasar Ingila a wannan watan.

dan wasa Dani Ceballos ne ya ci wa Arsenal kwallonta ta biyu da ya kai kungiyar wasan daf dana karshe a gasar cin kofin kalubale na FA Cup na bana, bayan doke kungiyar Sheffield United daci 2-1 ranar Lahadi.

Arsenal  ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan da kungiyar ta sayo wanda yafi kowa tsada a cikin tawagar, Nicolas Pepe a bugun fenareti, bayan da Chris Basham ya yi wa Aledandre Lacazette keta a da’ira ta 18..

Daga baya ne mai masaukin bakin, Sheffield United  ta farke ta hannun dan wasan ta  na gaba McGoldrick saura minti uku a tashi daga karawar sai dai bayan da alkalin wasa ya kara lokaci ne Arsenal ta ci kwallo ta biyu ta hannun Dani Ceballos wanda ke buga wa kungiyar wasannin aro daga Real Madrid.

“Samun nasara a wasanni biyu babban abune a halin yanzu idan muka duba yadda ake buga wasanni a wannan lokacin saboda haka da wannan nasarar nake fatan nasarar mu zara dawo domin mu ci gaba da samun nasara a dukkan wasannin mu na gaba” in ji Areta

Ya ci gaba da cewa “Arsenal babbar kungiya ce wadda take bukatar koda yaushe ace tana samun nasara a manya da kana nan wasanni sai dai yanayin da kungiyar ta shiga yasa hakan baya samuwa amma nan gaba zamu kawo gyara”

Wannan nasarar za ta kara wa tawagar ta Arsenal kwarin gwuiwa a shirin da take na shiga ‘yan hudun farko a gasar firimiya ko samun gurbin buga gasar Europa League a badi bayan an kammala kakar wasan bana.

Arsenal tana mataki na tara a kan teburin firimiyar Ingila da maki 43, kuma Arsenal din za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Norwich City wadda itama Manchester United ta doke ta a gasar ta FA a ranar 1 ga watan Yuli.
Advertisement

labarai