Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Sabon kwamishinan ‘yansanda Jihar Nasarawa Mohammed Uba Kura ya isa jihar tare da soma aiki nan take.
Kwamishinan wanda ya samu marhabin jami’an ‘yansanda da yin faretin musamman a hedikwatar rundunar ‘yansanda da ke Lafia, ya fara aiki ne ta hanyar ganawa da manyan jami’an ‘yansanda a ofishinsa.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala ganawarsa da manyan jami’an rundunar a jihar, sabon kwamishinan ya ce zai mayar da hankali ne kan yaki da manyan laifuka da ci gaba da tabbattar da kyakkyawar zaman lafiya a jihar.
Ya ce kan haka tuni ya sanar da manyan jami’an da ya gana da su da su rubanya kokarinsu wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na aikin dansanda.
Haka nan ya ce, shi da kansa zai kasance mai rangadi yana sanya ido a aikin jami’an domin tabbattar ba su wucce gona da iri.
Da yake yaba wa Sufeto Janar na ‘yansanda kan nada mukamin Kwamishinan ‘Yansanda Jihar Nasarawa, Kura ya yi kira ga mazauna jihar da su rinka bai wa jami’an tsaro hadin kai game da aikinsu na dakile muggan ayyuka da tabbattar da kyakkyawar zaman lafiyar al’umma.
A cewarsa, “Ko da kana dan jarida, ko dan siyasa, ko basaraken gargajiya da sauransu, ka kalli kanka a matsayin dansanda ta hanyar sa ido da samar da bayanan da za su taimaka wa ‘yansanda yaki da muggan ayyuka”.
Ya kara da cewa, “Idan ka ga ana aikata muggan ayyuka, ko da ba za ka iya zuwa kai tsaye ka fada min ko wani jami’i ba, kana iya sanar wa shugabanni da kake kusa da su, su kuma su sanar da mu domin daukar matakin da ya dace”.
Kafin nada shi kwamishinan ‘yansanda Jihar Nasarawa, Kwamishina Mohammed Uba Kura shi ne kwamandan kwallejin koyar da dabarun bincike na ‘yansanda da ke Enugu.