Nasarori Da Sojoji Su Ka Samu A Jihar Katsina – Birgediya Oyenka

Ya zuwa yanzu sansanin jami’an sojin Najeriya dake Faskarin jihar Katsina ya samu nasarori da dama a cikin wata guda daya shafe yana gudanar da ayyukansa.

Mukaddashin daraktan watsa labarai na rundunar Brigadier Janar Barnard Oyenka ya furta hakan yayin wata hira da manema labarai a Faskari.

Ya bayyana cewa sansanin wanda shugaban sojojin kasa ya kaddamar dashi  a ranar 6 ga watan Yuli wannan shekara domin tallafama kokarin rundunar operation hadarin daji a shiyyar arewa maso yamma.

Yace an kuma kaddamar da sansanin ne domin karshen aikace-aikacen yan bindiga satar shanu, garkuwa da mutane da kashe-kashe a shiyyar arewa maso yammacin kasar nan.

Rundunar ta gudanar da aikace-aikace daban-daban da suka danganci kwato bauna da kuma yin sintiri a jihohin Sokoto, Katsina da Zamfara wanda hakan ya taimaka wajen rage garkuwa da mutane, satar shanu, inda kuma aka kubutar da wasu da akayi garkuwwa dasu.

Sauran nasarorin da rundunar ta samu sun hada da kama wasu ‘yan bindiga da masu taimaka masu da bayanai da kuma masu hada gwiwa dasu.

Haka kuma sun samu nasarar kwto makamai, alburusai da kuma Babura da sauran kayayyakin yan bindiga a cikin wata daya daya gabata.

Brigadier Janar Onyenka a dukkanin aikace-aikacen da rundunar ta gudanar an kashe yan bindiga (80) inda a ka kwato dabbobi (143) da kuma bindiga kirar AK47 (633) da kwato wasu mutane da aka yi garkuwa dasu.

Kazalika ya ce rundunar ta samu nasarar lalata wani sansanin ’yan ta’adda da ke dajin Shimfida.

Exit mobile version