Nasarorin Da Hukumar NDLEA Ta Samu A Yaki Da Miyagun Kwayoyi  

Kwayoyi

Daga Mahmud Isa, 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi  NDLEA, karkashin jagorancin sabon shugaban ta, Burgediya Janaral Mohamed Buba Marwa mai ritaya tana ci gaba da samun nasarori da tun da aka kafa hukumar ba a taba samun makamancin hakan ba.

A cikin watanni uku kacal, hukumar NDLEA ta kama sama da mutane 2, 175 a kan laifukan safaran miyagun kwayoyi. An kama wadannan mutanen ne a lokacin da suke safarar kwayoyin a wurare daban-daban a fadin Nijeriya. Dukkan wadanda hukumar ta yi nasarar cafkewa tana samun su da muggan kwayoyi wadanda suke kokarin yadawa a cikin al’umma. Akalla ‘kilogram’ sama da miliyan biyu na miyagun kwayoyi ne hukumar ta samu nasarar kamawa tare da kwacewa a hannun masu safarar kwayoyin a cikin watanni uku. Miyagun kwayoyin sun hada da tabar wiwi, hodar iblis, methamphetamine, koken da makamantan su.

Wasu daga cikin wadannda aka kama sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun tsallake shiga hannun hukumar NDLEA, amma hakan ko kadan bai hana asirinsu ya tonu ba, inda hukumar take kwakulo kwayoyin a duk inda suka boye su tare da kama su nan take.

Okwonkwo Chimenzie, wani mai safarar miyagun kwayoyi ne zuwa kasashen waje wanda asirinsa ya tonu a ranar Lahadi, 4 ga watan Afrilu, lokacin da ya shiga hannun jami’an hukumar NDLEA a filin sauka da tashin jirage na Murtala Mohammed da ke birnin ikko a Legas. Jami’an NDLEA sun tsare Okwonkwo a yayin da suke binciken sa inda cikin kankanin lokaci bayan tilastawa da jami’an suka masa, ya tsuguna ya yi kashin kwayar koken wanda yawan sa ya kai ‘kilogram’ 1.750, wanda kuma kudinsa ya kai naira Miliyan 423. Kafin Okwonkwo ya shiga hannun hukumar NDLEA, hukumar ta kama wata mata ‘yar kasar Chadi mai suna Bibien Tarmadji a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja dauke da hodar ibilis a cikin al’aurarta wanda yawansa ya kai ‘gram’ 234.35.

Ko a watan da ya gabata, hukumar NDLEA ta kama dattijo mai shekaru 70 da miyagun kwayoyi yana safararsu zuwa ga ‘yan bindiga a daji. Wannan dattijo kafin dubunsa ya cika, shi ne babban dillalin kwayoyi na ‘yan bindiga dadi a dazukan Arewacin Nijeriya.

Wannan kadan ne daga cikin kamen da hukumar NDLEA ta yi a cikin watanni uku tun bayan da Janaral Buba Marwa ya zama shugabanta. Babu shakka martabar hukumar ya dawo kuma zuwa yanzu, masu karatu nasan sun shaida hakan saboda labaru da a kullum suke fitowa masu dadin ji daga hukumar ta NDLEA. Kazalika, nasan mai karatu ya sa hadarin da miyagun kwayoyi suke da shi ga al’umma, musamman idan ba a samu tsayayyun hukumomi irin NDLEA don dakile safarar kwayoyin a cikin al’umma ba.

Mu hadu a rubutu na gaba don samun karin bayani a kan aikace-aikacen hukumar NDLEA.

 

Exit mobile version