NASRDA Ke Da Hakkin Kaddamar Da Tauraron Dan Adam A Nijeriya – Buhari  

NASRDA

Daga Muhammad Maitela,

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake jaddada cewa hukumar gudanar da binciken sararin samaniya ta kasa (NASRDA) ita kadai ce hukumar da take da alhakin gudanar da bincike tare da kaddamar da tauraron dan Adam a Nijeriya.

Shugaban kasa ya bayyana hakan a babban taron da hukumar ta gudanar na kasa (NSC) a birnin Abuja, yayin da Buhari ya yi cikakken bayani dangane da ci gaban da ake dashi a kimiyya da fasaha, musamman abinda ya shafi gudanar da bincike, sadarwa, tare da kaddamar da tauraron dan Adam, aiki ne wanda ya kebanta da hukumar kula da sararin samaniya ta kasa. Har wala yau shugaban kasa ya bukaci shugaban hukumar hadi da ilahirin ma’aikatan hukumar su yi aiki da dokar NASRDA ta 2010.

Haka zalika kuma shugaban kasa ya yaba da kokarin hukumar NASRDA bisa nasarorin da ta samu a fannin kimiyya da fasaha a Afrika. Ya ce hukumar binciken sararin samaniyar ta taka muhimmiyar gudumawa wajen nuna kwarewa ta hanyar zayyana wa, ginawa tare da dora tauraron dan Adam a Nijeriya. Wadanda ya bayyana sun hada da NigeriaSat -1, NigeriaSat–2, NigComSat-1R tare da babban hobbasar kaddamar da tauraron NigeriaSat-D, wanda injiniyoyin Nijeriya suka zayyana tare da kera shi. Al’amarin da shugaba Buhari ya bayyana a matsayin nasara tare da sauya fasalin ci gaban Nijeriya a fuskar kimiyya da fasaha.

A nashi bangaren, Darakta Janar a hukumar NASRDA, Dr Halilu Shaba, ya yi karin haske dangane da tauraron dan Adam, samfurin NigeriaSat-2, wanda ya sanar da cewa har yanzu yana ci gaba da gudanar da aiki kamar yadda ya dace kuma ya na bayar da ingantattun bayanan da ake bukata bisa yadda aka tsara.

A hannu guda kuma, shugaban hukumar NASRDA ya yi karin haske dangane da ci gaban da suke samu tare da kudurin su na gina wa da kaddamar da karin sabbin tauraron dan Adam guda biyu, samfurin Synthetic Aperture Radar (Nigeria SAR -1) ta Optical Earth Observation Satellite (NigeriaSat-3).

Exit mobile version