NASU Ta Yi Barazanar Kulle Makaratun Nijeriya

NASU

Kungiyar ma’aikatan manyan makarantu waxanda ba malamai ba ‘Non-Academic’ (NASU) ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baabaa-ta-gani har sai gwamnati ta cire kura-kuran da suke jibge a cikin tsarin biyan albashi ta tsarin bai-xaya na IPPIS.

Mambobin kungiyar NASU dai sun kasaftu a jami’o’i, kwalajojin kimiyya, da kwalejojin ilimi da suke faxin kasar nan.

Har-ila-yau, kungiyar ta kuma shaida cewar a shirye take wajen xaukan dukkanin matakan da doka ya tanadar wajen ganin an tabbatar da adalci a tsakanin kowa da kowa wajen rabon naira biliyan arba’in (40b) da gwamnatin tarayya ta yi alkawarin baiwa kungiyar jami’o’i a matsayin alawus.

Da suke ganawa da ‘yan jarida a Abuja bayan kammala wani taron koli (NEC) na kungiyar, shugaban kungiyar ma’aikatan manyan makarantu da ba malamai ba, NASU na kasa, Makolo Hassan, ya shaida cewar tun lokacin da mambobinsu suka koma kan sabon tsarin IPPIS suka shan wahala sosai.

Ya ce, duk kokarinsu na ganin sun gana da Babban Akanta Janar na kasa domin gyara kura-kuran da suke akwai amma hakarsu ta gaza cimma ruwa.

Ya ce, daga cikin matsalolin da suka fuskanta sun haxa da zaftare albashi, karin haraji, rashin samun albashi a kan lokaci, babu biyan hakkokin karin girma da sauran matsalolin da suka gano a cikin tsarin IPPIS.

Ya tunatar da cewa, kungiyar ta shiga yajin aikin gargaxi na makonni biyu tare da sanya hannun yarjejeniya da gwamnati a ranar 20 ga watan Oktoban 2020 inda daga bisani aka umarci daraktan IPPIS da ya tabbatar da shawo kan matsalolin cikin mako biyu,

Ya ce, sun gano cewa gwamnati da ofishin da ke kula da sabon tsarin IPPIS ba su wani shirya na shawo kan matsalolin da suka gabatar musu ba, don haka ne ya ce “Ba mu da wani zabin da ya wuce mu tafi yajin aiki kwanan nan a faxin jami’o’i, kwalejin kimiyya da fasaha da suke faxin kasa, kwalejin ilimi har sai wani abun gaggawa ya faru na shawo kan matsalolinmu.”

Daga nan ya jawo hankalin gwamnatin tarayya kan batun kasafta kuxin alawus na biliyan 40 da cewa ya dace ne a yi adalci wajen wannan rabiyar.

Kungiyar ta nemi gwamnati ta shigo cikin lamarin nasu ko kuma su tafi yajin aikin da babu ranar dawowa sai an shawo mu su kan bukatunsu da matsalolin da su ke fuskanta.

Exit mobile version