Kungiyar Womanifesto, wacce ke wakiltar sama da ƙungiyoyin kare haƙƙin mata 350, ta buƙaci gudanar da bincike kan zargin cin zarafin jima’i da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Ƙungiyar ta buƙaci Akpabio ya sauka daga muƙaminsa nan take, a gudanar da bincike kan zargin, a gudanar da zaman jin bahasi na jama’a a kwamitin ladabtarwa na majalisa, da kuma barin duk wasu batutuwan da ke kotu su ci gaba da bin ƙa’ida.
- Matar Akpabio Ta Maka Sanata Natasha Kotu, Ta Nemi Diyyar Naira Biliyan 350
- Zargin Neman Yin Lalata: Ina Da Kwararan Hujjoji Akan Akpabio – Natasha
Womanifesto ta bayyana cewa yawan mata a muƙaman yanke hukunci a Nijeriya yana da matuƙar ƙaranci, kuma cin zarafin mata na ƙara ƙamari. Ta ce wannan batu ba zai iya shuɗewa ba tare da ɗaukar mataki ba.
Dr. Abiola Akiyode-Afolabi, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar, ta ce majalisa na fuskantar gwajin yadda take mutunta kundin tsarin mulki. Ta ce dukkanin ‘yan majalisa suna wakiltar al’ummarsu kuma dole a basu mutunci da martaba, ciki har da mata.
Ƙungiyar ta jaddada cewa majalisa na kan gwaji a idon duniya kuma dole ne ta ɗauki matakin tabbatar da adalci. Ta buƙaci a tabbatar da kare haƙƙoƙin mata da ‘yan mata, tare da tabbatar da cewa majalisa ta zama abin misali wajen kare ‘yancin mata daga cin zarafi.