NATO Ta Yi Kuskure Kan Fatan “Ci Gaba Da Dorewa” Ta Hanyar Wargaza Yankin Asiya Da Pasifik
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NATO Ta Yi Kuskure Kan Fatan “Ci Gaba Da Dorewa” Ta Hanyar Wargaza Yankin Asiya Da Pasifik

byCMG Hausa
2 years ago
NATO

Kungiyar tsaro ta NATO ta fara gudanar da taron kolin ta jiya Talata a kasar Lithuania. Baya ga babban jigon taron game da halin da ake ciki a kasar Ukraine, shugabannin kasashen Japan, da Koriya ta Kudu, da Australia, da New Zealand sun halarci taron a karo na biyu a jere, lamarin da ya sa batun samar da zaman lafiya na kungiyar NATO ya sake yin zafi. Kafofin yada labaran kasar Japan sun bayyana cewa, sakamakon adawar kasar Faransa, aka dage shirin bude ofishin hulda da kungiyar NATO na farko a yankin Asiya a kasar Japan, wanda tun da farko aka tattauna a taron kolin, har sai bayan kaka. Sai dai manazarta na ganin cewa, a karkashin jagorancin Amurka, aniyar kungiyar NATO ta fadada ikonta zuwa yankin Asiya da tekun Pasifik ba za ta canja ba.

A matsayin wani samfuri na zamanin yakin cacar baka, NATO ta kasance ginshikin tabbatar da mulkin Amurka tun kafuwarta. Tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka, kungiyar NATO ta fadada ikonta zuwa gabashi har sau shida bisa dabarun Amurka na “taimakawa Jamus da Faransa”, “da mayar da Rasha saniyar ware” da “gasa da kasar Sin “, wanda ya tada rikici tsakanin Rasha da Ukraine, da haifar da rarrabuwar kawuna a Turai, kuma tana ci gaba da fadada tasirinta zuwa yankin Asiya da Pacifik.

Yankin Asiya da Pacifik yanki ne mai fadi don neman hadin kai da ci gaba, ba kuma fagen da manyan kasashe za su yi gasa ba ne. Kungiyar NATO da Amurka ke jagoranta, tana son maimaita abin da ake kira “Kwarewar Turai” zuwa yankin Asiya da Pasifik, amma a hakikanin gaskiya, tana son kara haifar da rarrabuwar kawuna da rikici da yankin, amma jama’ar yankin ba za su yarda ba. NATO tana son “ci gaba da dauwama” ta hanyar wargaza yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma mutane masu son zaman lafiya a fadin duniya ba za su taba yarda ba. Kamar yadda Ken Stone, shugaban kungiyar da ke adawa da tayar da yaki ta kasar Canada, ya ce, NATO kungiya ce mai karfin fada-a-ji da Amurka ke jagoranta, bisa ga tsarin dokokin kungiyar, ta dade da yin hannun riga da ma’anar kafa ta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Ba Ma Son Ganin Abin Da Ya Faru A Kabul Ya Ci Gaba Da Faruwa

Ba Ma Son Ganin Abin Da Ya Faru A Kabul Ya Ci Gaba Da Faruwa

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version