Kungiyar tsaro ta NATO za ta shiga yakin da Amurka ke jagoranmta akan Mayakan IS, a Syria da Iraki. Matakin na zuwa kafin ganawar da shugaban Amurka Donald Trump zai yi da shugabannin mambobin kungiyar NATO a Brussels ranar Alhamis. Wasu majiyoyin Difolamsiyya ne suka tabbatar da cewa NATO za ta shiga yakin da Amurka ke jagoranta akan mayakan IS, bayan Trump ya bukaci kungiyar tsaron ta mayar da hankali ga yakar ayyukan ta’addanci.
Tuni sakararen harakokin wajen Amurka Red Tillerson ya bayyana fatan ganin NATO ta shigo cikin yakin da Amurka ta kaddamar akan IS duk da wasu mambobin kungiyar na dari-dari da abkawa cikin wani yaki a yanzu. Wasu majiyoyi daga Turai sun ce Faransa da Jamus sun amince da kudirin na Amurka kan shigowar NATO a yakin a ganawar da Trump zai yi da shugabannin kasashen na Turai
Rahotanni sun ce Jakadun kasashen mambobin NATO sun tsara matakan yaki da ta’addanci a taron da shugabannin na Turai za su yi da Donald Trump. Matakan kuma sun hada da fadada ayyukan jiragen leken asiri na NATO wajen yakar IS a Syria da Iraki. Wani labara mai kama da wannnan kuma, a ci gaba da samun koma baya da kungiyar IS din ke yi, Amurka ta ce ta yi barin wuta kan kungiyar ta’addancin, wanda ya hallaka da dama daga cikin mabiyanta a kasar Libiya.
Wasu hare-haren jiragen sama da Amurka ta kai a kasar Libiya sun hallaka karin mayakan IS, wanda wannan shi ne karo na biyu da Amurka ta kai irin wadannan hare-haren a wannan kasa ta arewacin Afirka ciki kasa da mako guda, tare da hadin gwiwar gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta GNA, sojojin Amurka sun kai hare-haren jiragen sama da aka auna kan ‘yan IS ranar Talata, inda mayakan IS din da dama su ka mutu, a cewar Rundunar Sojin Amurka mai kula da aiyukkan soji a Afirka, a wata takardar bayani da ta fitar.