CRI Hausa" />

Na’urar Tianwen-1 Mai Binciken Duniyar Mars Ta Yi Sauyin Wuri A Falakinta

Na’urar Tianwen-1 mai binciken duniyar Mars, ta yi sauyin wuri a kan falakinta a Litinin din, bayan nasarar da ta samu ta kasance na’urar farko kirar Sin da ta isa duniyar Mars.

Hukumar harkokin samajannati ta kasar Sin CNSA ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce an kunna injin na’urar da misalin karfe 5 na yammaci bisa agogon Beijing, domin baiwa na’urar damar kewaya falakinta a duniyar ta Mars. Kaza lika ana sa ran na’urar za ta gudanar da sauyin wurare, a kan falakin na ta kafin kaiwa ga zango.
Na’urar mai kunshe da sashen bincike, da na kewaye, da wurin sauka da motar zirga zirga, ta yi nasarar shiga falakin da aka tsara mata a duniyar Mars ne, a ranar 10 ga watan Fabarairun nan, bayan shafe kusan watanni 7 da barin doron duniya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version