Nazari A Kan Alhaji Muhammadu Gambu Mai Wakar Barayi

Alhaji Muhammadu Gambu Makadi ne mai fasahar gaske wakokinsa cike suke da balaga da azanci da salon Magana. Duk ga karin harshensa ya yi matukar tasiri cikin wakokinsa amma wannan bai hana manazarta da masu sha’awar wakokinsa fahimta ba tare da nazartarsu ba.

Haihuwarsa:

An haifi Alhaji Muhammadu Gambu a garin Fagada babba ta gundumar Aleiro karamar Hukumar Jega. Kamar yadda yadda yake cewa a wakarsa:

Muhammadu Rango anka haife shi

Yah hita yak ko amadoci

Ni Fadagawa sunka haife ni

Yawo yak kawo ni Jega

’Yat tunga kauyen Alelu.

An haife shi a wajejen shekarar 1949. Mahaifinsa Muhammadu Umar dan Malam Muhammadu Sani dukkan ninsu mutanen Fagada babba ne. Sannan mahaifiyarsa Malama Zalihatu abokanan haihuwarta su ke limancin garin Laga ta kasar Gwandu. Iyayen Muhammadu Gambu Kambarin Bare-bari ne. Sunan kauyen da yake shi ne Katanga a karamar hukumar Maiyama. Kasancewarsa dan malamai jikan malamai da kana yana fada a cikin wakarsa inda yake cewa :-

Jagora
Ko gidan giya nike
Dai dan Malam za a ce mini
Jikan Liman za a ce min
Don Liman yah haihi Gambu
Ka ga bai ci amanar mai kidi ba
Don ko ya aika ni Borno
Shekara ta goma sha hudu
:Sha hudu ko nar ratci sittin
Yau ga ni ina yawo da ganga.

Ko shi ma ya taba karatun allo duk da dai bai yi nisa ba waka ta janye shi.

Matarsa ta fari Hauwa’u ‘yar garinsu ce Fagada wadda mahaifiyarsa ce ta aura masa ita. Sannan ya kuma auren wata Kulu ta garin Badon hanya a karamar hukumar Wammako sannan ya auri wata Kulun a garin Ambursa matarsa ta hudu ita ce Luba ‘yar Mutanen Maiyama jihar Kabi. Gambu yana da yara shida maza uku mata uku.Sunansa Muhammadu na gaskiya masana suna ganin ya sami lakabin Gambu ne a bayan ya fada fagen waka.

Sana’arsa

Gambu ya tashi gidan ilimi don haka sai da aka saka shi makarantar allo ya budi ido da karatu kafin ya fara kowacce irin sana’a. Ya dan taba noma inda daga bisa ni ya koma farauta inda yake harbe-harben namun daji. Amma kafin nan ya yi sana’ar alawar suga ya yi sakar tabarma ya yi ya yi kirar rariyar tankade ta mata ya yi saka da kuma bugi na kamun kifi ya yi yawon kokawa da Karen mota da yaron mota da sauransu. Yana cikin wannan sana’a ta farauta ne ya din ga haduwa da barayi cikin jeji suna yin hulda. Inda a karshe har ya zama makadinsu. Amma yana taba wakokin ma su gari da na ‘yan siyasa.

Gambu bai gaji waka ba ta bangaren uwa ko uba ya tsinci waka ne sama ta ka ta silar farauta da huldar da ya yi da barayi sai kuma kasancewarsa dan caca na yankan shakku.

Bunza ya nuna cewa a tsarin fasahar Gambu wakokinsa na sata kari daya suke da shi. Hawa da saukar muryar daya ne sai dai kowane barawo a dora sunansa cikin wakar da irin bayanin da aka yi kansa. Muryarsa ta kidan sata na da dadi sosai Fasaharsa tsararriya ce salon hira ya fi yawa a cikin wakarsa. Gambu ya san sata ya san barayi , ya san kalmomin da ake fitar da sata a ji su a gan su.

Gambu ya yi wakokin barayi

Wakokin ‘Yan caca

Wakokin karuwai

Wakokin ‘yan tauri

Kidan gambara

Gambu a wakokinsa ba ya boyewa cewa yana yi wa barayi waka kamar yadda kowa ya san yana yi musu.

Ni am mai wakar barayi

Ko alkali na raga min

Don ko kayan kowa ban taba ba

Ya ce “ to fa Gambo lallai a bar sata garin ga….”

Gambu Fitacce ne a wakar barayi inda bayan ya kai kololuwar shahara amma lokaci guda ya ce ya tuba duk da yana ganin tun asali shi ba waka yake yi ba nazarin al’umma yake yi yana buga ganga ne domin shaidawa al’umma abin da take yi mai kyau ko maras kyau ko ta yarda ko kada ta yarda. Kenan a mahangar Farfesa Malumfashi Sata gaskiya ce nazarinta ma gaskiya ne. An ya an tuba da fadar gaskiya? Ashe ramin karya kurarre ne ? Ana kuma tuba da aikin adabi. Eey a’a Ana dai ajiyewa ko a yi ritaya ko murabus a huta don magada su ci gaba .

Watakil tuban Gambu daga baya ya yanke shawarar zai tuba don a cikin wakarsa yana cewa

Dud da ana yanke ni gobe

Dud da ana halbe ni gobe

Ba ni barin mugun kidan ga

Don ba tuba ni kai ba

Sai in mutuwa tad dauki raina

Ko in kuma Allah ya hukunta

Da alama Allah ne ya hukunta Gambu dai bai mutu ba, bai kuma tuba ba, ya dai bar waka haka nan bayan ya cika shekara 60 a doron kasa.

Duk da yadda Gambu ya shahara wajen wakar Barayi hakan bai hana shi yin wa’azi ba a wasu diyan wakar da yake yi.. A Kwai inda yake cewa a diyan wakarsa

Da an ka bude gida,

Sai nig ga dattijo

Ga shi da gemu ya yi saje

Nig ga hwarin gashi ga kai nai

Sai nic ce tuba Baba,

A sa ka cikin manyan mutane

Ka daina halin ‘yan yara-yara

Akwai kuma inda yake cewa:

Malam da zagin doka ga kai nai

Ya badan hoda yay gazal

Ba ta batun salla akai ba

Ba azumi ab ba ni so ba

Yawan sallah

Don hajji da barawo ba ni so nai

Tunda ba ta da lada tako arfa.

Haka ya na cewa

Duk mai fassara aya lahiya lau,

Shi yanke hukunci bangare nai,

Ya tabbata ya take sani nai

Gamonsa da Allah kaico kanshi

Alkalai na ga tausen ku

Na tuna kwana lahirarku

Ba ishe sauki za ka yi ba

An dauki amana an nika ma,

Ka kwashi garabasa ka kwanta,

Ba haka Allah ya hwadi ba,

Da zuwanmu kana gane kurenka.

Tuban Makadi Gambu abin farin ciki ne kwarai ya tuba a garin sokoto ya yin wani biki da ya je. Don da kansa ya tuba ba tilasta masa aka yi ba , ba kuma wuya ya gani ba, ba wata tsaka mai wuya ya shiga ba. Don haka tuban Gambu irin tuban da ake so ne wanda addini yake maraba da shi ne. Allah ya amshi tubansa ya gafarta masa kurakuransa amin.

Alhaji Muhammadu Gambo Fagada Allah ya yi masa rasuwa ranar Laraba 18/8/2016 da daddare bayan ya sha fama da rashin lafiya a garin maiyama da ke jihar Kebbi ya rasu yana da shekaru 67 ya bar mata hudu da ‘ya’ya da jikoki. Ba shi da magaji. Allah ya gafarta ma sa, amin.

 

Exit mobile version